SAKAMAKON TARON YI WA SHATA ADDU’A DA TUNA SHI NA RAN 18/6/2021 A KATSINA

ALHAMDULILLAHI an yi taro lafiya kuma ya yi armashi. Wanshekaren ranar taron, sai wasu abokaina su biyu suka same ni a ofis suka tsegunta ma ni akan zancen da na yi a wajen taron, na cewa ina son gwamnatocin tarayya da ta jihar Katsina su amshi gidansa na Funtuwa su mayar da shi wata babbar cibiya ta bincike, kamar dai yanda aka yi ma gidan Sardauna a Kaduna da kuma gidan Malam Aminu Kano a Kano. Shi ma zakin mawaka, Dodo na BS ya dace ya samu wannan gatancin.
Kafin ranar tunawa da Shata, a shekarar da ta gabata, na zanta da wasu masu ruwa da tsaki a cikin ‘ya’yan Shata akan a nemi gwamnati ta yi hakan. Sai suka ce ma ni ai suma suna son hakan, amma ai su, ba za su yi magana ba. Mu dai da mu ke fafutuka akan Shatan mu za mu yi yekuwa mu nemi gwamnet ta yi haka.

SHAWARA/ADDU’A (PRAYER/

1. Akwai bukatar a yi gidauniya (Endowment fund) akan Shata. A kira taro don hakan.

2. A nada kwamiti na amintattu don su tsara hakan, su aiwatar.

3. Da wannan gidauniya, za’a yi amfani da abin da aka samu a amshi gidan Shata. A sallami magada . A gyara gidan, ya koma daidai da irin cibiyar da ake so, ya Allah gidan adana kayan tarihi ko na assasa al’adun gargajiya, ko na kimiyyar siyasa. A yi shi daidai da irin wadannan cibiyoyi na biranen Duniya. Wannan za ya bayar da dama masu bincike ko masana ko masu yawon bude ido daga ko’ina cikin Duniya su zo Funtuwa gidan Shata. Hakan za ya ankarar da Duniya cewa yanzu an saki gidan don hakan.

4. Daga cikin abin da aka samu kuma za’a diba a gyara gidan su Shata da ke Musawa da kuma gidan sa mai suna gidan marke da ke gab da Musawa.

SABODA MI?

Saboda, gidan su na Musawa dai mahaifa ce wadda bai kamata a bar ta tarihi ya yi gaba da ita ba. Masu binciken tarihi daga sassan Duniya za su so a kawo su Musawa su ga inda aka haifi Shata don bincike. Amma gwamnati ta yi laifi da ta bari gidan na neman zama kufai.
Sannan, shi gidan marke gidan sa ne na gona da ke kusa da Dam din Shata inda ya ke jiye kadoji. Nan ya kan yi kasasuwa. Nan ya kan tara makada da mawaka irin su Musa Dankwairo suna yi masa kwanaki suna tama shi hira. Nan ya kan tara ‘yan dambe da masu kokowa suna tama shi hira. Saboda haka gidan ya shiga cikin tarihin da, yakamata a ce shi ma an barahi domin tarihi. Amma, abin takaici, ni Ali Kankara, na je Musawa bara (2020) sai na tarar an sayar da gidan. Wanda aka sayar ma wa kuma ya sare iccen marken da ke gab da gidan gonar. Sauran kufai (remnants) na gidan kuma mutumin ya rushe shi gaba daya. Yanzu, da mutum ya je wurin, babu abinda za ya gani ya tabbatar Shata ya taba yin rayuwa a wurin. Alhali kuwa, a lokacin rayuwar Shata, duk wakar da ka sani ya rera a Duniya, to ya taba yin ta a gidan marke.
Daga karsge, iyalan Shata suna da fillanci kwarai da nuna kawaici da yawan kauda fuska akan sha’anin Duniya. Kuma suna da kunya. Ba za su iya fitowa su yi kira ga gwamnet ta shigo ta amshi wadannan wuraren guda 3 ta gyara ba. Mu dai da ke fafutuka mu ya kamata mu shirya wata babbar inuwa mu nada kwamiti don yin hakan. Gwamnati kuma ba za ta yi haka ba sai ta ga an fara yi. Idan ta ga an yi to sannan za ta amshi wurin ta yi abin da ya dace a yi da wuraren. Amma matsawar aka zauna a haka, to watarana sai an wayi gari an je Musawa ba’a ga komi da za’a nuna na Shata ba.
Kishin abin ya sanya na yi wannan yunkuri.
Idan bangaren iyalan Shata da kuma bangaren masoya Shata masu ruwa da tsaki sun aminta da hakan, to sai a tattauna a kira taron tsara kwamiti daga kowanne bangare. Kuma a yi abin da sauri.

Aliyu Ibrahim Kankara
Mawallafin littafin Shata, Talata, 22/6/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here