Advert
Home Sashen Hausa Saida tsohon ginin Ma'aikatar yaɗa Labarai ta Jihar Katsina: Inada Shakku akan...

Saida tsohon ginin Ma’aikatar yaɗa Labarai ta Jihar Katsina: Inada Shakku akan Adalcin Gwamna Masari….Ra’ayin Aminu Salisu

Saida tsohon ginin Ma’aikatar yaɗa Labarai ta Jihar Katsina: Inada Shakku akan Adalcin Gwamna Masari….Ra’ayin Aminu Salisu

Ra’ayin Aminu Salisu

Kafin Intafi kai tsaye ga abinda naji kuma ya tada mani Hankali, zanso inyi tuni ga Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari cewa: a dokar ƙasa, Idan Mutum yazama Gwamna a Jiharsa to shine Lamba ɗaya a jihar, ta kowane Fanni na gudanarwa,

Maigirma Gwamna A matsayinka na Gwamnan Jihar Katsina, kaine Shugaban Rundunar tsaro ta jiharka, kaine shugaban kula da lafiya na jiharka, kaine shugaban kula da Ilimi na jiharka, kaine shugaban kula da bada kariya ga duka al’uma da duk wani Gini na jiharka,

Bisa Shedar da muka iya samu akanka, Gwamna Kai mutum ne mai son cigaban jiha da Al’umar jiharka, bisa wannan hali naka mai kyau yasa wasu miyagu suke yaudararka suna cutatawa jiharka da al’umarka dama Siyasar ka,

Mai girma Gwamna jiharka tana daga cikin jihohin da baƙo ke tsoron ya shigo saboda Rashin tsaro,

A ƙoƙarinka na samar da tsaro munsani babu irin fafutukar da bakayi ba, a yanzu zan’iya cewa har ƙarfinka ya ƙare ta fuskacin tsaro,

Maigirma Gwamna bisa ƙoƙarin na ka ne na samar da tsaro yasa kasanya wata Doka, wadda ta maida Ofisoshin jami’an ‘yan Sanda a katsina, cibiyar Kasuwanci,

Mai girma Gwamna Idan baka saniba, to kasa ayi bincike, cibiyoyin tsaro na ‘yansanda a jihar katsina, (bama kamar cikin birni) yazama Dandalin Saye da sayarwa, ma’ana Idan aka kama mai laifi, komin kankantar Laifin Idan baka da kuɗi, za’aimaka Sharri a haskawa duniya a bidiyo ace kana taimakawa ɓarayi,

Idan kuma kanada Kuɗi komai girman Laifinka, za’a haskaka da bidiyo amma ace kasayi Bidiyon ko a nunama Duniya,

Maigirma Gwamna Ko kasan cewa Dokar da kasanya ta Kama Babura da Masu NAPEP dayawa daga cikin jami’an tsaro sunyi kuɗi ta wannan hanyar…..? Idan baka saniba ka bincika.

Kamar yanda na fadi ana amfani da sonka ga Al’uma ana ha’intarka, Maigirma Gwamna abinda nayi kwalli dashi daga jiya zuwa yau, ya tadamani hankali, ance ka saidama wani dan’kasuwa Ginin tsohuwar ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar katsina,

Maigirma Gwamna nasan kunsani cewa wannan gini yana daga cikin abubuwan tarihi da Alfahari na jihar Katsina, mi wajen yayimaka ne shin bakasan ganin wajen ne, ko mike faruwa?

Titin da Ma’aikatar take Titi ne babba a cikin Birnin Katsina da yake bukatar faɗaɗawa, saboda Cunkoso, idan har ba’a faɗadashi ba mi zaisa a cinkusheshi, ta hanyar saidama Kamfani Ma’aikatar da nan gaba sai tazama wajen buɗe ido da yawon shaƙatawa domin samar da kuɗin shiga ga jihar? Alhali duk dan Katsina yasan yanda wannan Kamfani ke haddasa cinkoso busa hanyar!!

Kamfanin dake bukatar Babban Fili a waje domin faɗadawa, (koda yake naji har kyautar Fili, Gwamnatin Katsina tayi masa a a titi mai yalwa, miyasa baka sanya ya maida Mazaunin sa a wajen ba?

Mai girma Gwamna duk wani waje mai Daraja a Katsina Idan har Gwamnatinka ba cefanar dashiba, a yanzu tana akan hanya, wannan ba ci gaba bane, Irin wannan ne ke haddasa Cunkoso wanda zai iya haifarda danasani, ko kuma wata Gwamnatin tazo tayita yima al’uma Rusau suna Allah ya isa.

Mai girma Gwamna Kaine fa kace. “Idan aka ga mun yi abinda ba dai-dai ba, a faɗa mana mu gyara, saboda ni har wurin mai gadin Gidana ina ɗaukar Shawara kowane Mutum na da matuƙar Muhimmanci da Baiwar da Allah yayi masa”

Da wannan nake takaitawa, dafatan saƙon ya isa kunnen Maigirma Gwamna, ya gane cewa Tabbas ana ɓata masa Siyasa, kuma idan bai gyara ba, waɗanda ya ɗauka masoyansa sune zasu dunga zaginsa a gaban Kotun EFCC. Da na gaba…..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: