Sai mai sakamakon First Class kadai za mu dauka aikin koyarwa – Gwamnatin Tarayya
Daga, Ibrahim M Bawa
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa daga nan zuwa 2021 masu kwarewa a kan fannin koyarwa da suka fita da sakamakon fintinkau na First Class kadai za a dauka aikin a duk fadin Nijeriya.
Gwamnatin ta kuma kara da cewa, amma za ta duba wadanda suka fita da sakamako na biyu wato 2.1 domin tabbatar da cewa an inganta harkar ilimi ta daukar kwararrun malamai tun da farko.
Babban Sakataren ma’aikatar ilimin tarayya Sonny Echonu, shi ne ya bayyana hakan wajen duba yadda jarabawar kwararrun malamai PQE da Teachers Registration Council of Nigeria, TRCN, ke shiryawa a duk fadin kasar nan
Malamai 17, 602 dake cikin jihohin Nijeriya 36 gami da babban birnin tarayya Abuja ne suka shiga cikin zana jarabawar.