Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba batun kudi ne ke zuwa mulki ba.

“Na zama gwamnan Kano lokacin dana tumbatsa, lokacin da zan iya rike wannan kujera saboda nayi shugaban karamar hukuma, sakataren karamar hukuma, kwamishina na tsawon shekaru 6 a lokacin mulkin soja, na yi aiki a Babban birnin tarayya Abuja kusan shekara 20 har na zama darakta, na yi Mataimakin Gwamna na shekara 8 ga shekara 6 a matsayin Gwamnan Kano.

Gwamnan ya ce ya samu gogewa tun daga tushe kuma yasan yarda za’a tattara kudade da sarrafa su.

DAILY TRUE HAUSA ta samu wannan labari ne a cikin wani dan takaitaccen faifan bidiyo mai dauke da muryar gwamnan da Jaridar RFI ta wallafa a shafinta na Facebook.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here