SABUNTA TITIN ZUWA TASHAR JIRGIN ƘASA TA IDU A ABUJA

#GaskiyarLamarinNijeriya..ko kunsani NG

Ko kun san cewa, a bara Gwamnatin Shugaba Buhari ta gyara titin da ke kan hanyar zuwa tashar jirgin ƙasa ta Idu da ke Abuja duk da kasancewar a cikin shekarar a na tsaka da annobar cutar Korona?

A ranar 30 ga Yuni, 2020, ne, Babban Sakataren Ma’aikatar Birnin Tarayya Abuja ya jagoranci tawagar ma’aikatar, inda suka duba yadda ake gudanar da aikin, wanda aka mayar da titin na kankare a karon farko a tarihi.

Titin ya tashi daga cikin gari har zuwa Gosa, wajen da ake jibge shara.

Wannan aiki ya gwada yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta taɓa gazawa ba wajen gudanar da manyan ayyuka, don kyautata rayuwar mafi yawan ‘yan Nijeriya!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here