Sabon Shugaban Chadi na ganawa da Buhari

Sabon Shugaban Chadi Janar Mahamat Idriss Deby ya ziyarci shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Janar Mahamat Idriss Deby ne yake jan ragamar kasar tun bayan mutuwar
mahaifnsa a watan da ya gabata.

Shugaba Buhari ne ya tarbe shi kafin su shiga yin wani taron sirri.
Kawo yanzu, babu bayani kan abin da taron nasu zai mayar da hankali a kai.
Kafin rasuwar mahaifin nasa, Najeriya da Chadi sun kulla alaka wajen yaki da
ta’addanci.

Marigayi Idris Deby ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji a wata fafatawa da yan
tawaye a watan Aprilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here