Sabon Sarkin Zazzau ya gana da gwamna Elrufai a ofishin gwamnati

A karon farko bayan naɗa shi sarki, Mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli ya kai wa gwamnan Kaduna ziyara.
Sarki Bamalli ya kai ziyarar ne tare da ƴan majalisar masarautar Zazzau zuwa ofishin gwamnan Elrufai.

A ranar 7 ga watan Oktoba aka naɗa Sarki Bamalli a matsayin sarkin zazzau na 19.
Ya maye gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki.
Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920.

