Sabon jirgin yaƙin da Najeriya ta saya ya isa ƙasar

Copyright: NAF
Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karɓi jirginta na biyu mai saukar ungulu ƙirar Mi-171E da gwamnatin tarayyar ƙasar ta saya daga ƙasar Serbia.
A wani saƙo da rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa wannan ne jirgi na biyu mai saukar ungulu ƙirar Mi-171E da gwamnatin tarayyar ta saya.
Rundunarta bayyana cewa wannan ne jirgi na 23 da rundunar ta saya tun a 2015.

Copyright: NAF

Copyright: NAF