Biyo bayan yarjejeniyar da aka shiga tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da kuma Shahararren Ɗan kasuwar nan mai Kampanin Green House Katsina wato Alh. Shehu Na- Maska akan gina wannan katafariyar Ma’aikata shi kuma abashi tsohuwar Ma’aikatar dake cikin garin Katsina Yau dai aiki ya kammala.

Sabon ofishin na Katsina State Teachers Service Board da Kamfanin Green House ya gina musu karkashin wannan yarjejeniyar tsakanin kamfanin na Green House da Gwamnatin jihar yana yana cikin farfajiyar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Katsina mai suna Garba Ja Abdulkadir Complex dake Dandagoro akan hanyar Katsina zuwa Kano.

Idan dai ba’a manta ba Ma’aikatan Hukumar suna ta ƙorafin rashin samun sukuni wajen gudanar da ayyukan su a tsohon matsugunnin nasu dake cikin gari a baya, da samuwar wannan wurin yanzu zamu Iya cewa Aiki kam yanzu babu kama hannun Yaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here