Home Sashen Hausa Sabon farmaki: Dalibai sun tsere daga wata Makaranta a Zamfara

Sabon farmaki: Dalibai sun tsere daga wata Makaranta a Zamfara

A zamfara dalibai sun tsere da kafarsu a wata makarantar sakandare dake unguwar Damaga, karamar hukumar Maradun dake jihar Zamfara yayinda yan bindiga suka kai sabon farmaki.

Yan bindigan sun dira garin ne ranar Laraba kan babura suna harbin kan mai uwa da wabi.

An ce Akalla mutane 13 suka rasa rayukansu kuma an yi awon gaba da Shanu.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta samu ji daga wani mazaunin garin, Musa Damaga inda ya bayyana abinda da faru.

Sun dira garin misalin karfe 1 na rana kuma suka fara harbin mutane. Dalibai na daukan darashi a makarantar sakandaren dake garin amma yayinda suka ga yan bindigan, dukkansu suka arce daga aji,” cewar Musa Damaga.

“Yanzu da nike muku magana, an gano gawawwakin wadanda aka kashe kuma an kammala shirin jana’izarsu.”

Yayinda aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce kawai a bashi lokaci.

Dalibai Sun Tsere Lokacin Da ‘Yan Bindiga Suka Sake Kai Farmaki Jihar Zamfara, Sun Hallaka 13

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here