Kowace kabila na da bata gari amma saboda tsanar da wasu sukawa Buhari duk abinda aka yi sai suce Fulanine – Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie

Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ta bayyaba cewa dorawa Fulani duk wani laifin abinda aka yi son tada Fitinane.

Ta bayyana hakane a matsayin martani ga kalaman babban lauya, Femi Falana inda ya zargi gwamnatin tarayya da baiwa Fulani Makiyaya Kariya.

Tace sam abinda wasu da basa son shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke yi bai kamata ba. Tace saboda Shugaban kasar Bafulatanine duk abinda aka yi sai a daurawa Fulani saboda kiyayya.

Tace tana kira ga masu irin wannan hali su kwantar da hankulansu bamu da kasar data wuce Najeriya. Su jira shekarar 2023 ta zo sai su yi amfani da kuri’unsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here