*SABO MUSA; MUTUMIN DA AKA HARAMTA WA RIJISTA A APC*

_Mu’azu Hassan_
_@ Jaridar Taskar Labarai_

Binciken Jaridar Taskar Labarai, ya tabbatar cewa, an haramta wa mutane da yawa a Jihar Katsina yin rijista da jam’iyyar APC. Daga ciki har da Alhaji Sabo Musa Hassan.

Mun bincika a jam’iyyar ta Karamar Hukumar Katsina da kuma mazabarsa ta Kudu 111, an fada mana cewa, an ba su umurni kai tsaye kar wanda ya kuskura ya yi wa Sabo Musa rijista a matsayin dan jam’iyyar APC.

Laifin da ake zargin Sabo Musa da aikatawa shi ne, halartar wani taro a Kano mai suna APC Pressure Group. Taron da aka kare martabar gwamnatin APC, amma aka yi kira da a yi gyara a tafiyar da tsarin shugabancin jam’iyyar.

Taron da ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP suka kira da wani salo na tallar jam’iyyar APC. Sabo Musa ne ya fi kowa magana a taron.

Taskar Labarai ta bi duk wadanda suka je taron, ta samu tabbacin dukkaninsu an yi masu rijista, wasu ma har gida aka same su aka yi masu. Cikin su har da wani Attajirin da aka ce shi ne ya dau nauyin taron.

Taskar Labarai ta bi sunayen jiga-jigan taron, duk sun tabbatar mata da cewa an yi masu rijista ta APC, wasu har rokon su aka yi aka ce don Allah su zo domin ana jiran su.

*WA YA HANA A YI WA MASA RIJISTA?*

Duk wadanda jaridar nan ta yi magana da su, sun tabbatar mana cewa, umurni ne daga uwar jam’iyya ta Jiha.

Bincikenmu ya wanke Gwamna Aminu Bello Masari daga wannan kwamacalar. “Gwamna mutum ne mai hakuri da yafiya, da sake ba mutum dama ya gyara kuskurensa”, in ji majiyar tamu.

Bincikenmu ya hada sunayen mutanen da suks cutar da Gwamna da siyasarsa da kokarin keta masa mutunci, amma ya yafe masu, yanzu ana tare.

“Hakurinsa da yafiya sun sa yakan mai da ‘ya’yan wasu nasa, kamar yadda yakan mai da makiyi masoyi. Don haka babu ruwansa”, in ji majiyar tamu.

Bincikenmu ya gano cewa wata tsohuwar gaba ta cikin gida ce ake son a kawo ta cikin jam’iyya, wanda ya kamata manya su sanya baki.

Mun gano cewa tsakanin Sabo Musa da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Malam Shittu S. Shittu, akwai wata tsohuwar cikakka a tsakaninsu duk da kuwa gidansu daya. Ana iya cewa Uba daya, Uwa ko da tasa suke, amma duk haka ba sa ga-maciji da juna.

Wasu da jaridar nan ta yi magana da su, sun zargi Malam Shittu S. Shittu da kokarin neman ganin bayan Sabo Musa ta hanyar yin amfani da matsalar da ya shiga.

Wasu kuma na ganin ana neman kulle bakin Sabo Musa ne don a raunana wani dan jam’iyyar da ke neman takarar Gwamna a 2023 da Sabo Musa ke tare da shi, kuma yake ma wa baya.

Duk masu neman takarar Gwamna a 2023, suna zargin Malam Shittu S. Shittu da karkata ga wani bangaren da ke son takarar.

*WAYE SABO MUSA?*

Sabo Musa ya fara siyasa ne sama da shekaru 30 da suka wuce. Ya rike mukamai a jam’iyyu daban-daban da aka yi a baya, yanzu kuma shi ne SA Restoration ga Gwamnan Katsina.

A kwanakin baya suka kafa wata kungiya mai suna APC Pressure Group, wadda suka ce manufarta kawo gyara a cikin shugabancin jam’iyyar APC.

A taron nasu sun kare martabar gwamnatin APC, amma sun soki shugabancin jam’iyyar, a kan haka jam’iyyar ke neman yi masu abin da wasu ke zargin bita-da-kulli ne.

*RIKICIN KATIN A WASU YANKUNAN*

Za mu fara kawo maku rikicin da ke ruruwa a wasu Kananan Hukumomin Katsina a kan ba da katin na zama dan jam’iyyar APC daga gobe Asabar 20/2/2021 insha Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here