A ranar Asabar 16/10/2021, aka zabi shugabannin jam’iyyar Apc na matakin Jiha bayan an zabesu ta hanyar sasanci, sannan daga bisani aka rantsar dasu a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin garin Katsina, wanda Kwamishinan Shari’ah kuma Babban Lauyan Jihar Katsina Barr. Ahmed Usman El-Marzuq ya jagoranci rantsar dasu.

Sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar Apc na Jihar Katsina da aka rantsar sun hada da!

(1) Shugaban Jam’iyyar na Jiha – Alh. Sani M. Ali
(2) Mataimakin shugaba – Alh. Bala Abu Musawa
(3) Sakataren Jam’iyyar na Jiha- Malam Shitu S. Shitu
(4) Mataimakin Sakatare – Alh. Umar T. Mustapha

(5) Ma’ajin jam’iyyar – Babangida Yardaje
(6) Mataimakin Ma’ajin jam’iyyar – Alh. Tanimu Maigari
(7) Sakataren tsare, tsare – Aminu Yusuf maigoro
(8) Mataimakin Sakataren tsare, tsare – Abdu Dan Yaro
(9) Shugaban Matasa Jam’iyyar – Alh. Hamza Mamman Sheme
(10) Mataimakin shugaban Matasa – Murtala Shehu

(11) Mai Binciken kudi na Jam’iyyar – Bishir Sabi’u Maitan
(12) Mataimakin mai binciken kudi – Ibrahim Mamman
(13) Shugabar mata ta Jiha – Haj. Jamila Salman
(14) Mataimakiyar shugabar mata ta Jiha – Saratu Ibrahim
(15) Mai bada shawara akan Shari’a – Barr. Nasiru Umar Wagini
(16) Mataimakin mai bada shawara akan Shari’ah – Elder Balele Kurfi

(17) Shugaban Matasa na shiyyar Katsina – Isma’il Usman Yandaki
(18) Shugaban Matasa na shiyyar Funtua – Sama’ila Garba
(19) Shugaban Matasa na shiyyar Daura – Murtala Abdullahi

(20) Shugabar mata ta shiyyar Katsina ta Tsakiya – Ladidi Umar
(21) Shugabar mata ta shiyyar Funtua – Haj. Aisha Yahaya
(22) Shugabar mata ta shiyyar Daura – Sadiya Abdullahi

(23) Mataimakin shugaba na shiyyar Katsina – Alh. Yahaya Asasanta
(24) Mataimakin shugaba na shiyyar Funtua – Lawal Abdullahi
(25) Mataimakin shugaba na shiyyar Daura – Hon. Mudansiru Mati K.

(26) Sakataren kudi na Jam’iyyar- Ali Mamman
(27) Mataimakin Sakataren kudi – Aminu Abdu
(28) Wakilin Masu Bukata ta musamman – Dahiru Gambo
(29) Jami’in hudda da jama’a na Jam’iyyar – Alh. Shamsu Sule
(30) Mataimakin Jami’in hudda da jama’a – Habibu Gilma
(31) Sakataren walwala na Jam’iyyar – Hon. Shafi’u Abdu Abdu Duwan
(32) Mataimakin Sakataren walwala na Jam’iyyar – Ibrahim Bala
(33) Ibrahim Danjuma

(34) Ex-offio 2 – Haj. Nasara Abubakar Gora
(35) Ex- offio 3 – Engr. Abba Yusuf
(36) Ex-offio 4 – Shu’aibu Sani Dutsi.

A cikin jawabin Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari bayan rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar na Jiha, ya jawo hankalinsu da suji tsoron Allah a bisa jagoranci da aka basu, Gwamnan ya cigaba da cewa” da kyakykyawar manufa aka zabo ku, idan kunyi abun kirki damu a ciki, amma idan kunyi akasin haka babu mu a ciki. Daga karshe Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya tayasu riko.

Tunda farko da yake gabatar da jawabinsa shugaban Kwamitin shirya zabukan jam’iyyar na jihar Katsina Alh. Muntari Lawal ya yabama Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari akan yadda ya yi kokari wajen ganin jam’iyyar Apc a Jihar Katsina ta tafi tsintsiya daya Madaurinki daya, daga karshe ya bayyana cewa” daga yau aikin Kwamitin da ya jagoranta don shirya zabukan jam’iyyar tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi da Jiha yazo karshe. Shugaban Kwamitin shirya zabukan daga uwar jam’iyyar Apc ta kasa karkashin jagorancin Hon. Ali Dattuwa Kumo ya jagoranci shirya zaben.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, shugaban majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango, Alh. Dahiru Bara’u Mangal Shugaban tafiyar jam’iyyar Apc a Jihar Katsina, tsohon Gwamnan Jihar Borno Rdt. Col. Abdulmuminu Aminu, Dr. Dikko Umar Radda shugaban hukumar (SMEDAN).

Sauran sun hada da, Ministan sufurin Jiragen sama Sanata Hadi Sirika Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, Sanata mai wakiltar shiyyar Katsina Sanata Kabir Abdullahi Barkiya, Sanata mai wakiltar shiyyar Funtua Sanata Bello Mandiya, ‘yan majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, ‘yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina, yan majalisar Dokoki ta Tarayya da suka fito daga Jihar Katsina.


Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
16 October, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here