WhatsApp: Sabon sauyin kafar sadarwar ya bar baya da ƙura

WhatsApp

WhatsApp ya ja hankalin masu amfani da shi a duniya inda suka wayi gari da sabon saƙo daga kamfanin sadarwar na wayoyin salula, wani sabon salo da ba a saba gani ba.

WhatsApp ya turo da saƙon ne ga miliyoyin masu amfani da shi a ranar Laraba 27 ga watan Janairu.

Saƙon ya ja hankali musamman a Twitter inda aka dinga muhawara kan WhatsApp tare da ƙirkirar maudu’in #WhatsApp.

Tun da dama WhatsApp na fuskantar ƙalubale kan sabon tsarinsa da ya shafi bayanan sirri da ya ce ya ɓullo da shi wanda kuma yake buƙatar masu amfani da kafar su amince ko ya toshe.

Miliyoyin mutane ne suka yi ƙaura daga WhatsApp zuwa wasu ire-irensa saboda gudun shiga rayuwarsu ta sirri

Shafin ya ɓullo da wasu sabbin sharuɗɗa ne da suka shafi bayanan sirrin mutane.

Miliyoyin masu amfani da shafin a fadin duniya ne suka yi wa wannan shiri tutsu, har ma suka koma amfani da wasu shafukan masu hamayya da Whatsapp kamar Signal da Telegram.

A kwanan nan ne Telegram ya ce yawan masu amfani da shi sun haura miliyan 500, kuma ya ƙara samun jama’a daga masu ficewa daga WhatsApp

Sakon WhatsApp da mutane suka wayi gari da shi
Bayanan hoto,Sakon WhatsApp da ya tsoratar da mutane

Sakon da WhatsApp ya turo ya shafi ƙarin bayani ne kan sabon tsarinsa inda ya ce sauyin bai shafi bayanan sirri da sakwanni da kiran da mutane ke yi ba, suna cikin tsarin kariya na end-to-end encryption.

WhatsApp ya ce ya bullo da sabon tsarin ne saboda kasuwanci domin ba da damar cinikayya a shafukan da aka buɗe domin kasuwanci musamman tsakanin WhatsApp da sauran kafofin sadarwa da suke gida ɗaya Facebook da Instagram.

Sannan a saƙon na Whatsapp ya ce zai ci gaba da sanar da masu amfani da shi kan sabbin tsare tsarensa.

WhatsApp ya tsorata mutane

Masu amfani da WhatsApp da dama sun ce sun yi tunanin kutse aka yi masu.

A tsarin WhatsApp sai mutum ya ajiye lambar mutum a wayarsa zai iya ganinsa amma kuma abin da ya tsorata wasu shi ne ganin bayanan WhatsApp da kansa ba tare da saninsu ba ko amincewarsu.

Wasu sun ce WhatsApp ne ma ya yi masu kutse, yayin da kuma yake neman su fahimci sabon tsarinsa.

@Tomilola_19 ta ce: WhatsApp yanzu a WhatsApp status ruɗani cikin ruɗani, da farko na yi tunanin matsala ce ta samu waya ta lokacin da na ga wannan saƙon.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

@LachickWavela tambaya ta yi cewa; shin wai ita ce kawai ta ji tsoro lokacin da ta saƙon WhatsApp? cikin murmushi, baki a buɗe da zufa, sai da wasu suka fara buɗewa kada ace wani mugun abu ne.

@jamoh_mwa ya wallafa saƙon WhatsApp a shafinsa na Twitter inda ya ce: Wannan ya tsorani #WhatsApp

Wasu sun tsorata ne kan yiyuwar tatsar bayanansu zuwa Facebook saboda alaƙarsa da WhatsApp.

Me ake cewa a Twitter?

Da dama na caccakar WhatsApp ne yayin da kuma wasu suka mayar da saƙon WhatsApp din almara.

@FolaWalker123 ya ce yana mamakin a yi masa kutse kuma a ce an damu da sirrinsa. Sai Mark Zuckerberg

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

@ahmedyhasan ya ce: Ta yaya WhatsApp zai tabbatar da kare sirrin mutane.

@EzeJohhn kuma saƙo ya rubuta wa shugaban Facebook Mark Zuckerberg, mai mallakin WhatsApp inda ya ce: Idan har za ka iya kutsowa ta taga ka shigo WhatsApp status kuma ba ka cikin waɗanda na ajiye lambobinsu, Ina mamakin inda zaka iya shiga.

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

@leykstar ya yi amfani da maudu’in WhatsApp tare da cewa an yi wa mutane kutse ba da saninsu ba, bayan kuma tabbatar da kare bayanan sirrinsu.

Kauce wa Twitter, 4

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Wannan layi ne

WhatsAPP dai ya tsawaita wa’adin da ya ba masu mu’amala da shi na amincewa da sabon tsarinsa.

Ya tsawaita wa’adin amincewa da sharaɗin daga ranar 18 ga wannan wata zuwa 15 ga watan Mayu, domin abokan hulɗarsa su samu damar yin nazari, ko kuma ya daina aiki a wayoyinsu idan sun ƙi amincewa.

A ƴan tsakanin da WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin, ya yi hasarar miliyoyin masu amfani da shafin.

Kuma ana ficewa WhatsApp saboda tsoron mika bayanansu ga Facebook, inda miliyoyin mutane a duniya ke ci gaba da rungumar wasu hanyoyin sadarwa na salula kamar Telegram da Signal don kauce wa sabbin sauye-sauyen WhatsApp.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here