Majalisar zartaswa ta jiha a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince da bada kwangilar chanza na’urorin da suke daidaita kyawun ruwa daga cikin madatsar ruwa (Dam) a daidai lokacin da famfuna za su jawo shi zuwa tashar tace ruwan dake Ajiwa.

Su wadannan na’urori da ake kira clarifies, ana hada su a can kasan ruwan, daidai kan bakin bututun dake fito da ruwan.

Baya ga wadannan na’urori, wannan kwangila ta sama da Naira Miliyan Dari Tara, ta hada da duk wasu ayyuka da suka rage a wannan babbar tashar ruwa da take a Ajiwa. Kuma ita ce kwangila ta karshe da a bada domin dawo da wannan tasha sabuwa, domin kuwa duk wani inji ko na’ura dake wannan tasha an canza shi da sabo baya ga kare karen da aka yi, musamman ta bangaren samar da wutar lantarki da kuma yawan ruwan da tashar za ta samar.

Wannan na kunshe ne cikin wani jawabi da Kwamishinan albarkatun ruwa Alhaji Musa Adamu Funtua ya yi wa manema labaru.

A daya bangaren, Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin Noma Dokta Abba Abdullahi, ya bayyana wa manema labaran cewa gwamnatin Jiha ta samar da ton dubu ukku (3,000) domin karfafa wa masu noman rani wajen kyautata wannan sana’a tasu. Haka kuma gwamnatin ta dauri aniyar tabbatar da duk wani bangare na gandun dajin jihar nan ya dawo hannun gwamnati daga hannun wadanda suka wawure shi tare kuma da daukar matakan hana afkuwar hakan nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here