Rundunar Yansandan Jihar Kano tayi Nasarar chafke Barayin Waya….

Mai Magana da yawun Rundunar Yansandan DSP Haruna ne ya gabatar da Matasan gaban manema labarai, dukkanin su Yara ne kanana daga Shekaru Goma Sha Tara zuwa Shekaru Ashirin da Tara.

Matasan suna tare Jama’a ne ko a Masallatai ko Gidan Kallon kwallo ko Wuraren Bukukuwa na cikin Gari su yi amfani da wuka wurin kwatar wayoyin Jama’a, Wani lokacin kuma a cikin Kekenapep ko Adaidaita Sahu ko kurkura.

Ko a jiya Laraba dai masu ƙwacen wayar sun kashe wani ɗalibi mai suna Muhammadu Rabi’u inda sukayi awon gaba da wayarsa ta hannu.

Kazalika Rundunar ta kama manya Manyan masu safarar Miyagun kwayoyi a jihar wanda dukkanin su Zaa gurfanar dasu a gaban ‘kuliya manta sabo bayan an kammala Bincike.

Allah ya Shiryar Mana da zuri’a ya karemu dukkan Miyagun Ayyuka Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here