Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai suna Yusuf Abdullahi Dan Asalin Kauyen Kagara ta Karamar Hukumar Charanchi.

Kakakin Rundunar SP.Gambo Isah shine ya gabatar da Dan Bindigar ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar dake Katsina.

Idan Masu karatun The Fact 24 basu manta ba a cikin shekararda ta gabata a ranar 1-6-2020 Yan Bindiga dauke da manyan makamai suka yi dirar mikiya a garin Yantumaki inda suka hallaka Uban Kasar da wani mai gadin gidansa.

Kamar yadda Dan Bindigar ya bayyana sun Halaka Hakimin Yantumaki ne bisa dalilin cewa yana neman daya daga cikin yan kungiyarsu mai suna Shamsu akan aikata wani laifi na fashi da Makami.

Yace Shamsu shi da kanshi shine ya hallaka Hakimin da Bindiga a yayinda daya daga cikin mutane su hudu Masu dauke da bindiga ya kashe mai gadin.

The Fact 24 ta tsinkaye shi yana mai cewa sauran wadanda suka aikata kisan Hakimin a halin yanzu suna daji inda nan ne maboyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here