Home Sashen Hausa Rundunar ‘Yansanda sun kama ‘yan ta’adda 1,503 da barayin shanu 526 a...

Rundunar ‘Yansanda sun kama ‘yan ta’adda 1,503 da barayin shanu 526 a Katsina…

Rundunar ‘Yansanda sun kama ‘yan ta’adda 1,503 da barayin shanu 526 a Katsina…

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta gurfanar da mutane Dubu Daya da Dari Daya da Goma Sha Shidda 1,116 a gaban kuliya bisa zargin aikata ta’addanci a jihar cikin shekarar Dubu Biyu da Ashirin 2020.

Rundunar ‘yansandan ta ce yawansu na daga cikin mutane 1,503 da ta yi nasarar kamawa ta ke kuma zargi da aikata ayyukan ta’addanci a fadin jihar.

Da ya ke jawabi a taron manema labarai na karshen shekarar Dubu Biyu da Ashirin 2020 a Katsina, kwamishinan ‘yansandan jihar CP Sanusi Buba, yace ‘yansanda sun kuma kama ‘yan fashi da makami Dari Biyu da Sittin da Bakwai 267 Kuma duk an maka su kotu.

Yace duk a cikin Shekarar ta Dubu Biyu da Ashirin 2020, ‘yansandan Katsina, sun kuma yi nasarar kama mutane Dari Biyar da Ashirin da Shidda 526 da ake zargi da satar shanu, tare da ceto shanun sata Dubu Daya da Dari Ukku da Sittin da Shidda 1,366 da tumaki Dubu Daya da Dari Biyu da Goma Sha Daya 1,211 da awaki Dari Biyu da Saba’in da Daya 271 da jakuna Hudu 4.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here