Advert
Home Sashen Hausa RUNDUNAR YAN' SANDAN JAHAR KATSINA TA CHAFKE MASU GARKUWA DA MUTANE DA...

RUNDUNAR YAN’ SANDAN JAHAR KATSINA TA CHAFKE MASU GARKUWA DA MUTANE DA MASU BAIWA YAN’ TA’ADDAN BAYANAN SIRRI

Hassan Male Kankara

@ katsina city news

Rundunar Yan’ sandan Jahar Katsina ta samu nasarar kama masu garkuwa da mutane, da barayin shanu da masu baiwa Yan ta’adda bayanan sirri, gami da rukakkun Yan ta’adda.

Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar Katsina SP Gambo Isah, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya wakana a Shelkwatar Rundunar, a madadin Kwamishinan Yansandan Jahar Sanusi Buba.

A cewar SP Gambo Isah, rundunar ta samu nasarar kama rikakken dan ta’adda mai suna Bala Abdu da akafi sani da Medele Mai Shekaru 40, da Kuma Halliru Tukur Mai Shekaru 24, dukkanin su, sun kasance yan kauyen Dunkula na Karamar Hukumar Safana.

SP Gambo Isah yace an samu nasarar kama su ne, bayan sunje Kasuwar Runka domin sayar da ragon da suka sata, inda suka tabbatar wa da rundunar cewa sun kasance suna aikata ta’addanci da satar Shanu a Safana da kewayanta.

Kakakin rundunar yace biyo bayan bayanan sirri, rundunar ta kuma kama Masu baiwa Yan ta’adda bayanan sirri, da suka hada da; Mani Yahaya Mai Shekaru 38, da Isuhu Usman mai Shekaru 35, dukkanin su Yan Kauyen Tsaskiya ta Karamar Hukumar Safana.

SP Gambo Isah, ya kara da cewa, an dai zarge su ne da bayar da bayanan sirri ga Sansanonin Yan ta’adda guda biyu, da suka hada da Ya’u da Mallam Aibo dukkanin su, suna zaune a dajin Rugu, inda suka taba gudanar da ta’addanci a Kauyen Tsaskiya da Ummadau na Karamar Hukumar Safana.

Kamar yadda Isah ya shaidawa manema labarai, rundunar Yan’ sandan ta kuma kama wani Aminu Abdulrazak Mai Shekaru 30 dake Unguwar Tudun Yan’ Lihidda, dauke da jarkoki 66 a wata mota kirar ‘Peugeot 504′ a garejin Kofar Guga, Wanda ya kasance yana kaiwa Yan ta’adda Man Fetur a Daji.

Acewar SP Gambo Mai laifin yace ya sayo Man Fetur din ne daga wani Saminu Rabiu, Manajan Zirga-zirga na gidan Man AK Mai Kwai.

A lokacin da rundunar Yan’ sandan ke gudanar da bincike, dukkanin wadanda ake tuhumar sun tabbatar da cewa sun aikata laifin.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: