Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wani matashi dan shekara 37 mai suna Abdulkareem Muhammed dauke da lita 32 na man fetur a cikin ledodin polythene guda uku sannan aka boye su a cikin jakar matafiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar.
Ya ce jami’an da ke sintiri sun kama wanda ake zargin a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya.
“Wanda ake zargin daga nesa zaka iya cewa yana tafiya ne da tufafi a cikin jakar tafiya da yake dauke da ita, amma da jami’an bincike suka bincika sai suka gano buhunan ledojin polythene guda uku dauke da lita 32 na fetur, in ji shi.
Ya kuma kara da cewa an kama wasu karin wadanda ake zargin da suka bi hanyar Katsina zuwa Jibiya domin safarar fetur zuwa ga ‘yan fashi a da zuzzukan kuma an gurfanar da su a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here