Rundunar NSCDC a Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wasu mutane su biyu da ake zargi da safarar tabar wiwi zuwa Jihar Katsina.

Kakakin Rundunar DSC.Muhammad Tukur Abdara shine ya gabatar da mutanen biyu da ake zargi ga manema labaru.

Kamar yadda DSC Abdara ya bayyana,wadanda aka chafke din sun dauko tabar wiwi din ne daga jihar Legas a cikin wata babbar mota da ta dauko Kaya zuwa Jihar Katsina.

Direban motar dai an bashi umarnin cewa idan ya iso Zaria zai dauki wani mai suna Sunday wanda shine zai hannanta tabar wiwin ga mai ita a garin Daura.

DSC Abdara yace a halinda ake ciki direban motar ya gudu kuma jami’an hukumar na cikin nemanshi.

Kamar yadda Mr.Sunday yace,ana bashi kudi naira dubu hamsin a duk lokacinda ya kawo irin wadannan kayayyakin.

Daga bisani Hukumar ta NSCDC ta hannanta mutanen biyu da ake zargi ga Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kasa dake nan Katsina domin cigaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here