Rundunar sojin Najeriya ta ce binciken ICC zai karya wa sojoji ƙwarin guiwa

Rundunar sojin Najeriya ta mayar da martani kan binciken da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta ce za ta yi kan laifukan yaƙi da aka aikata a Najeriya.
A ranar Juma’a ne mai babbar mai shigar da ƙara ta ICC Fatou Bensouda ta ce za ta yi bincike kan Boko Haram da sojojin Najeriya kan cin zarafi da laifukan yaƙi da aka aikata a shekarun da aka kwashe na rikicin Boko Haram.
Sai dai a sanarwar da wallafa a shafinta na Facebook, rundunar sojin Najeriya ta ce wannan zai yi tasiri ga karya ƙwarin guiwar sojoji.
“Babu shakka irin wannan bayani na tunzurawa na iya janye hankalin sojojin Najeriya saboda tasirinsa na karye masu ƙwarin guiwa. Zai haifar da mummunan tasiri ga ƙwarin guiwar da sojojin suke da shi da kuma aikin soja ga ƴan Najeriya da haifar da koma-baya ga dukkanin ayyukan tsaro a ƙasar.”
Sai dai sanarwa ta ce babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi kira ga sojojin su yi watsi da abin da ya kira abin da zai ɗauke hankalinsu tare da yin kira ga sojojin kada su damu ko karaya da matakin.
Rundunar ta ce matakin ICC na zuwa ne bayan rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta fitar tana neman a gudanar da bincike kan “ta’asar da sojojin Najeriya suka aikata.”