Rundunar ta bayyana yadda tayi Nasarar chafke Barayin masu fasa Gidajen Mutane suna satar masu Babura, a ranar 6/6/2021, bisa ga Rahotannin sirri rundunar ƴansandan tayi Nasarar chafke Barayin wadanda suke addabar cikin birnin Katsina da kewawaye.

Rana ta baci ne dai ga wani Matashi mai suna Nura Salisu, Ɗan kimanin Shekaru Ashirin da Takwas 28 dake Unguwar Gambarawa cikin garin, Katsina, barawon wanda ya ƙware wajen ƙetara gidajen Mutane yana masu Sata, ya kutsa Gidan wani Ibrahim Datti dake Unguwar Farin yaro Inda ya sace mashi mashin ƙirar Jincheng – Lucky, Ja wanda ba’a yi ma Rajista ba.

Yayin Gudanar da bincike bayan da aka kamashi ya tabbatar da aikata laifin da ake tuhumar shi da aikatawa ya kuma bayyana cewa kimanin Babura Guda Shidda ya sata kuma yana kaisu ne wajen Muhammadu Abdullahi, Ɗan kimanin Shekaru Ashirin da Tara 29 dake zaune a Sabuwar Unguwa Katsina, wanda ƙwararren bakanike ne yana sauyama baburan da aka sata fenti a sauya kalarsu ta yadda ba za’a iya ganewa ba.

Haka nan kuma Ɗaya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Nura Salisu ya amsa cewa ya saci mashin din Yaquba Rabi’u a Unguwar ta Gambarawa ya kuma saidawa wani bakanike.

Yayin binciken Ƴansanda sun samu wani Mashin din ƙirar jincheng Rubber, wanda shima bayada Rajista, da kuma wani Mashin din ƙirar boxer motorcycle shima marar Rajistar, an kuma same su da plate numbers – KTN 357 UX da AGL 453 QL – Lagos kazalika da Logo na plate numbers a Gidan bakaniken da ake zargi Muhammad Abdullahi.

Shima wani da ake zargi mai Suna Hassan Sani ‘dan kimanin Shekaru Ashirin da Biyu 22 dake Unguwar Dan bedi katsina bincike yasa an kamo shi tareda Mashin ƙirar Jincheng Rubber, Baƙi mai Lamba KAT 964 QA wanda ake zargin na sata ne, gaba daga kimanin babura Babura Hudu ne Rundunar Ƴansandan ta samu wajen wadanda ake zargin ana kuma cigaba da bincike akan Lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here