Rundunar ƴan sanda tayi nasarar cafke wani mai safarar makamai ga ɓarayi daji.

Rundunar ƴansanda tayi nasarar cafke wani ƙasurgumin mai safarar makamai zuwa ga ƴan tadda a katsina

Rundunar Yansandan Jahar Katsina tayi Nasarar Chafke wani Mai Safarar Alburusai ga Barayin Daji.

Hukumar ta Yansanda tayi Nasarar harbe wani Matashi Dan kimanin Shekaru Talatin da Biyar Mai suna Abubakar Haruna a kafa akan hanyar shi ta Shiga daji dauke da Alburusai Dari Sidda a cikin Mashin kirar Boxer.

Yansandan bisa Jagorancin Area Commander na Dutsinma sune sukayi wannan Kamu, an dai harbi wanda ake zargin a kafa lokacin da yayi niyyar gudu, wanda hakan yayi sanadiyyar Mutuwar shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here