Advert
Home Sashen Hausa Rufe Otel Din Gabby Na Katsina Zai Kawo Raguwar Badala A Tsakanin...

Rufe Otel Din Gabby Na Katsina Zai Kawo Raguwar Badala A Tsakanin Matasa Maza Da Mata – Cewar Dan Majalissa Albaba.

Dan Majalissa dake wakiltar Karamar Hukumar Katsina a Majalissar Dokokin Jihar Alhaji Ali Abubakar Albaba,ya bukaci Majalissar akan ta gaggauta bada umarnin rufe Otel din Gabby dake nan cikin garin Katsina.

Alhaji Ali Abubakar Albaba ya gabatar da wannan kudiri ne gabanin gabatar da rohoton Kwamitinda Majalissar ta kafa domin yin bincike akan harkokinda ake gudanarwa a Otel din.

Kamar yadda Dan Majalissar ya bayyana,Otel din na Gabby yana bada gagarumar gudummuwa wurin gurbacewar tarbiyar matasa da mata musamman masu kananan shekaru.

Alhaji Ali Abubakar Albaba yace Otel din tayi kaurin suna ta fuskar fasikanci da badala a tsakanin matasa baya ga bada gudummuwa ta fuskar karuwar shaye-shaye a tsakanin matasa.

Saga nan sai ya bukaci Majalissar akan tayi gaugawar bayar da umarnin rufe Otel din kafin kwamitinda Majalissar ta kara ya kammala bincikensa akan wurin.

Ya nuna damuwa akan cewar al’umma da kansu suka kawo mashi korafin iron badalarda ake a wurin India suke roko akan Gwamnati ta bada umarnin rufe Otel din na Gabby.

Majalissar Dokokin dai a halinda ake Ciki dai ta aike da wannan kudiri ga bangaren zartaswa akan bukatar rufe Otel din.

Masu Karatun The Fact 24 minene ra’ayinku akan wannan kudiri na Dan Majalissar?.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...