Ruɗani a Majalisar Wakilan Najeriya bayan ‘yan PDP sun koma APC

Ruɗani a Majalisar Wakilan Najeriya bayan 'yan PDP sun koma APC

Ruɗani a Majalisar Wakilan Najeriya bayan ‘yan PDP sun koma APC

‘Yan majalisar tarayya Najeriya

An sha hatsaniya a zaman Majalisar Wakilai ta Najeriya a yau Laraba yayin da wasu ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar PDP mai adawa suka sanar da komawa APC mai mulki.

Jaridar The Nation ta ruwaito Ephraim Nwuzi mai wakiltar Mazaɓar Etched/Omuma daga Jihar Rivers da kuma David Abel mai wakiltar Mazaɓar Gashaka/Kurmi/Sardauna daga Jihar Taraba, sun sanar da komawarsu APC ne cikin wasiƙun da suka rubuta wa Kakakin Majalisa Femi Gbajabeamila.

Sai dai, yayin da While Nwuzi yake zauren, shi kuma David Abel ba ya nan, abin da ya sa Gbajabeamila ya ce sai ya halarci zaman sannan za a karɓi wasiƙar tasa a hukumance.

Nan take kuma Shugaban Masu Rinjaye, Honarabul Alassan Ado Doguwa ya karɓi Nwuzi zuwa jam’iyyar ta APC.

Sai dai, mambobin jam’iyyar PDP sun yi watsi da matakin ‘yan majalisar sannan suka buƙaci Kakakin Majalisa ya ayyana kujerunsu a matsayin waɗanda babu masu su.

Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu ya koka cewa Kundin Tsarin Mulki ya ce sai in an samu rikici a cikin wata jam’iyya sannan mambobinta ‘yan majalisa suke da damar fita daga cikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here