Mu’azu Hassan @Katsina City News

A cikin shekarar 2019 aka bude gidan rediyon VISION FM a Kano, wanda aka nada Adamu S. Ladan a matsayin Janar Manaja, shi kuma ya dau ma’aikata da kansa bisa tsarin aikin da yake son shiga gasar tsere wa tsara da dimbin gidajen rediyo masu zaman kansu da ke Jihar.

“Da zai amshi gidan rediyon shi ne ya zo da tsarin daukar ma’aikatansa, ya yanka masu albashin da zai ba su da tsarin gudanarwar shi. Muka ce ya yi mana tsada. Ya ce zai nemo kudin da zai tafiyar da gidan rediyon da kansa da zai yi wa koya albashi, kuma ya samar da riba,” in ji daya daga cikin Daraktocin gidan rediyon.

VISION FM yana da wasu rassa a wasu Jihohi, don haka nan da nan sunansa ya fantsama a Kano, hadi da aikin da kwararrun ’yan jarida da aka dauka aiki suka yi. Kafin a je ko’ina ya zama daya daga cikin gidajen rediyon da ake saurare sosai a Jihar.

Ana cikin haka, kwatsam a watan mayu na 2021, sai wasu ma’aikata 13 a gidan suka fitar da wata takardar manema labarai suka sanar da sun ajiye aikinsu. Wadanda suka sa wa takardar hannu sun hada har da Janar Manaja na gidan, Malam Adamu S. Ladan da sauran jiga-jigan da aka bude gidan rediyon tare da su.

Sun ba da dalilai na rashin biyansu albashi da wasu hakkokin da ya kamata a ba su, amma ba a ba su ba, zargin da Hukumomin gidan rediyon suka musanta, inda suka ce su wadanda suka fitar da sanarwar kamata ya yi a sallame su ne, amma aka ba su damar su ajiye aikinsu cikin mutunci, sai suka mayar da abin arzikin da aka yi masu zuwa na tsiya, bata suna da kuma yamadidi.

A cikin watan Oktoba na 2021, Adamu Ladan da abokan ajiye aikinsa sun rubuta wa Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano takarda a kan ya kwato masu hakkinsu na albashi da suke bin VISION FM.

A cikin takardar da suka bai wa Kwamishinan, wadda jaridun KATSINA CITY NEWS suka gani, sun bayyana cewa sun rubuto ne saboda kungiyoyi irin su ta ’yan jarida (NUJ) da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, sun yi iyakar kokarinsu, amma sun kasa. Don haka suke neman ’yan sanda su shiga cikin maganar.

A takardar mai shafuka hudu da kalmomi 1058, sun yi zarge-zarge masu yawa a kan wadanda suka mallaki gidan rediyon na VISION FM da kuma babban Daraktansa, Umar Farouk Musa da ke Abuja.

A watan Nawumba 2021, Lauyan su Adamu S. Ladan, H.M Ma’aruf &co, ya rubuta wasika zuwa ga Hukumar EFCC da ke da ofis a Kano yana neman Hukumar ta kwato wa wadanda yake tsayawa hakkokinsu na albashi da sauran hakkokinsu da suke zargin VISION FM Kano ya rike ya ki biyan su.

A wasikar mai shafi daya, Lauyan ya yi ikirarin cewa wadanda yake karewa suna bin Hukumar VISION FM Kano, zunzurutun kudi har Naira miliyan takwas da dubu dari biyar da naira ashirin.

Hukumar VISION FM sun fitar da wata sanarwa, inda suka karyata duk zarge-zargen da ake masu, suka kuma ce a kan lamarin albashin ma’aikata na Kano za su bincika, kuma za su biya duk wani mai hakki, hakkinsa. Suka ce rikicin ma’aikata ba VISION fm ba ce farau, amma duk in ya taso binciken cikin gida kan warware shi, ba yamadidi ba, kuma sun dau matakin na bincikawa.

Binciken farko da aka fara yi suka samu hannun shugabannin gidan rediyon VISION FM Kano da sarrafa kudin shiga na gidan rediyon ba yadda ya dace ba, kuma suka mika koken su ga Hukumar ’yan sanda a ranar 13/11/2021.wasikar da jaridun katsina city news suka gani.

A wasikar da suka rubuta wa ’yan sanda, VISON FM sun yi korafi da zargin batan dabo da dimbin miliyoyin Naira suka yi a hannun shugabannin gidan rediyon karkashin adamu ladan, suka kuma nemi ’yan sanda su binciki ladan a matsayinshi na shugaba. Yan sanda Sun gayyace shi a kan koken a ranar 15/12/2021, inda ya rubuta masu nasa jawabinshi.

Hukumar VISION FM ta Kano ta kafa wani kwamitin binciken kudi da ya gudanar da cikakken bincike a kan duk kudaden da gidan ya samu tun daga 2019 zuwa 2021. Nawa aka samu? Ya aka sarrafa kudaden?

Sannan aka kafa wani kwamiti da ya kira duk wadanda suke da korafin albashi su bayyana gabansa domin a tantance su da kudin da suke bi, in an gama samun tabbaci da tantancewa a biya su hakkinsu.kamar yadda wani jami,i a gidan vision FM ya fada ma jaridun katsina city news

Rahoton mai binciken kudi ya fara gano wasu abubuwan da aka yi ba daidai ba, sannan ya gano gaskiyar kudin da ya kamata a ba duk wadanda suke bin bashi, kamar yadda takardun binciken da jaridun KATSINA CITY NEWS suka gani. Duk wadanda suke da korafi sun halarci zaman kwamitin ban da Adamu Ladan da mutum daya.

A ranar 9 ga watan Disamba 2021, Lauyan kamfanin VISION FM mai suna Bashir Nasiru &co, ya rubuta wa Lauyan wadanda suka ajiye aiki amsar wasikar neman hakkin wadanda yake karewa da ya rubuto, tare da kwafin da ya aika wa Hukumar EFCC.

A wasikar mai shafi daya, Lauyan VISON FM ya ba da amsar cewa, bayan bincike da tantancewa da suka yi, sun gano wadanda yake karewa suna bin gidan rediyon bashin Naira miliyan daya ne da dubu dari uku da saba’in da daya da Naira dari biyu (1,371,200.00).

A wasikar Lauyan VISION FM ya rubuta cewa a kan wasu kudade da wadanda yake karewa suke bukata, tun da sun ajiye aikinsu ba tare da ba da shela ba, kuma sun bar gidan, a doka yanzu sun rasa wadannan hakkokin tun da su ba ma’aikatan gidan ba ne.

A wasikar suka zayyana sunan kowa da abin da yake bi, suka kuma rubuuta cewa da zarar Hukumar gidan ta gama bincikenta na kudade za su biya kowa hakkinsa kamar yadda suka tabbatar.

A dai watan na Disamba Hukumar VISION FM ta gayyaci duk tsaffin ma’aikatan da suke bin bashi, aka kuma tantance su, bayana sun rubuta takarda suka amshi kudinsu.

Cikin mutane 12 da suka sanya hannun a waccar takardar bakwai suka bayyana suka sanya hannu na amsar kudin da suka amince shi suke bi, suka kuma sanya hannu ba maganar shari’a, kamar yadda takardun da jaridun KATSINA CITY NEWS suka gani. Uku kuma ba sa bin bashin ko Sisi Kobo.suma sun ce basu ja da duk wata maganar Shari a .kamar yadda daya daga cikin su ya fada ma katsina city news

Cikin ma’aikata 12 da suka yi korafin, bakwai sun rubuta ba su da ja, uku ba sa bin ko Kobo, wadanda suka rage daga Adamu Ladan, sai mataimakinsa, wadanda Hukumar VISION FM suka ce ba za a biya su ba, sai an kammala binciken da ake yi. Za su biya su hakkinsu su ma in akwai wani hakkinsu a VISION FM a kan su su nema.

A rahoto na biyu na bincike da aka yi, wanda aka aika wa Shugaban gidajen rediyon VISION FM da ke Abuja mai taken: Rahoton binciken kudi na gidan rediyon VISION FM Kano daga watan Janairu zuwa Disamba na 2019-2020 da kuma Janairu 2020 zuwa Mayu 2021.

Rahoton ya bi kudin shiga da aka rika tarawa wata-wata, ya kuma bi wadanda rahoton tattara kudi da aka rika aika wa hedikwatar VISION FM da ke Abuja. Ya bi tallar da aka rika sakawa da shirye-shiryen da ake biyan kudi da aka rika sakawa. Rahoton ya kuma bi duk yadda aka rika shigar da wasu kudaden da kuma sarrafa su.

Daga karshe rahoton ya gano kudade masu yawa da ba su shiga cikin asusun VISION FM ba. Ya kuma gano wasu kudaden da aka yi amfani da su ba ta hanyar da ta dace ba. Misali rahoton ya ce, daga Janairu-Disamba 2020, tashar ta samu kudade har Naira miliyan 38,434,587, amma miliyan 10,094,800 aka ga shigar su cikin ajiyar kamfanin, kamar yadda rahoton ya rika lissafo abin da ya gano a bincikensa.

A bincikenmu mun gano wasu daga cikin ma’aikatan da suka sanya hannu a takardar ajiye aikin, yanzu sun sake komawa aikinsu. Mun yi magana da daya daga cikinsu wadanda bai son a fadi sunanshi inda suka ce matsalar da aka samu ta rashin samun bayani ingantacce ne daga hedikwatar VISION FM din da ke Abuja da kuma Kano.

“Abin da ya faru shi ne sakon da Manajojin Kano ke fada mana daban, abin da muka ji bayan tantancewa da maganar keke-da-keke kuma daban. Don haka za mu iya cewa an samu rashin fahimtar sako, ko rashin isar da shi yadda yake ne”, in ji biyu daga cikin wadanda muka yi magana da su da suke cikin wadanda suka sa hannu a wasikar ajiye aikin a baya.

Duk kokarin da muka yi na jin ta bakin Malam Adamu Ladan a kan matsayinsa dangane da wannan rikicin, abin ya ci tura, bai ba mu amsar sakon da muka tura masa ba.

Sai dai wani da ya yi ikirarin shi Lauyansa ne, ya ba da amsa kamar haka; “Adamu Ladan ya yanke shawarar ba zai sake magana a kan matsalar VISION FM Kano ba. Dalilinsa shi ne maganar tana wajen ’yan sanda da kuma Hukumar EFCC da kungiyar ’yan jarida (NUJ) ta Jihar Kano, kuma wasu manyan mutane sun sa baki. Kuma Adamu yana ganin mutuncin wasu Daraktocin da suka mallaki kamfanin na VISION FM.”

Sakon ya ci gaba da cewa; “Adamu Ladan yana da cikakken bayanai a rubuce na duk zaman sa a matsayin Shugaban gidan rediyon, bai jin tsoron ya je gaban kowane kwamiti mai zaman kansa don ya ba da nasa bahasin da takardu da bayanai ingantattu.”

Lauyan ya ci gaba da cewa Adamu ya shekara 33 yana aikin jarida, ya rike mukamai daban-daban, a tarihinsa ba a taba samun sa da laifin aikita rashin gaskiya ba, kuma bai taba sata ko karkatar da kudi inda ba su dace ba.

Lauyan ya ce yana son duk rubutun da za a yi a sani, yanzu maganar tana gaban Hukumomi daban-daban, kuma a yi taka-tsantsa da bata suna don kauce wa daukar matakin shari’a.
Lauyan ya cigaba da cewa baka yanke ma mutum hukunci da rahoton cikin gida kuma binciken bai daya.
Don haka a jira matsayar kotu ko kuma rahoton wani bangare mai zaman kansa.inji lauyan.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here