Advert
Home Sashen Hausa RIKICIN JAM'IYYAR PDP A KATSINA: AN RUFE KOFAR SULHU ..A...

RIKICIN JAM’IYYAR PDP A KATSINA: AN RUFE KOFAR SULHU ..A kyale kotu ta yi hukunci_

.A kyale kotu ta yi hukunci_

Mu’azu Hassan

@ Katsina City News

Zaman da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP suka yi a ranar Lahadin da ta gabata 5/9/2021, ya zartar da rufe duk wata kofar sulhu a kan rikicin da jam’iyyar ke ciki tun bayan zaben shugabannin ta.

Rikicin, wanda wasu da suka kira kansu ‘yan PDP a-gyara suka shigar da kararraki daban-daban a kan shugabannin da aka zaba, kuma har wata kotu da yanke hukuncin da ya ba su gaskiya, amma wadanda aka zaba din suka daukaka kara zuwa Kaduna.

Domin nemo hanyar gyara, shugabannin na PDP da ‘yan PDP a-gyara sun yi wasu tarruka na neman mafita da kuma daidaitawa.

Taron ya kai ga har aka rubuta wasu takardun yarjeneniya da aka ba Editocinta Jaridun nan suka karanta. Abin da kawai ya rage sanya hannu.

A ranar Lahadin da ta gabata 5/9/2021 aka kira taron masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyya na Jiha, inda aka gabatar masu da matakan da ake ciki na sulhu da ‘yan PDP a-gyara.

Wadanda suke wurin suka ce Shugaban jam’iyyar, Alhaji Salisu Majigiri shi ne wanda ya fara jawabi, inda ya yi maganar ta sulhun da abin da ta kunsa a dukunkune, wanda mutane suka kasa fahimtar inda aka dosa da kuma abin da yake nufi.

Sai da Sanata Yakubu Lado Dan Marke, ya yi bayani filla-filla, sannan aka fara muhawara a kan maganar.

Magoya bayan Sanata Yakubu Lado Dan Marke, suna son a yi sulhu da ‘yan PDP a-gyara kamar yadda wata takarda yarjejeniyar da muka gani ta kunsa.

Su kuma masu goyon bayan shugabannin jam’iyya suna son a bari kotu ta yanke hukunci.

Daga karshe dai rinjayi mutanen Yakubu Lado Dan Marke masu son a yi sulhu a wajen kotu, kamar yadda daya daga wadanda suka halarci zaman ya ba mu labari.

Bayan yanke shawarar a bari kotu ta yi hukunci, shugabannin zaman sun gana Wakilin PDP a-gyara, Alhaji Lawal Rufai Safana, inda suka shaida masa matsayar da aka dauka ta cewa babu maganar zaman sulhu, yanzu a PDP sai dai a bari kotu ta yanke hukunci a kan rikicin da ake ciki. Shi kuma ya ce zai isar da sakon da aka kawo masa ga sauran membobin PDP a-gyara.

Daya daga cikin ‘yan PDP a-gyara, ya tabbatar wa da jaridunmu cewa, za su yi zama su dau matsaya guda a kan lamarin nan gaba kadan.

Katsina City News

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: