RIKICI YA DABAIBAYE SHUGABAN APC NA KATSINA

_Suleman Umar @Katsina City News_

Rikici da cece-kuce sun dabaibaye Shugaban jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, Alhaji Shittu S. Shittu.

Kwanan nan Hukumar Kwastam ta dira kan wani kamfaninsa mai suna MASLAHA MOTORS, inda suka debi wasu motoci suka tafi da su bisa zargin an shigo da su za a siyar ba tare da an biya masu haraji ba.

Daga baya MASLAHA MOTORS sun kai wa Hukumar Kwastam din karin wasu motoci guda biyar da Hukumar ba ta samu damar tafiya da su ba a lokacin da aka kai wancan samamen.

Wata majiya a Hukumar ta Kwastam ta ce, dukkanin motocin da aka tafi da su da wadanda aka kai masu daga baya sun sanya masu tambarin motocin da aka kwace saboda an shigo da su ba bisa ka’ida ba.

A ranar da aka kai samamen, babban Darakta a kamfanin na motocin MASLAHA, Alhaji Muhammadu, ya yi hira da manema labarai kai tsaye ta kafar sadarwar yanar gizo, inda ya yi kaca-kaca da Hukumar Kwastam din, wanda ya yi zargin ana masu bita-da-kulli da kuma makircin siyasa.

A hirar Muhammadu da manema labarai ya ce, ana son cin fuska da mutuncin Malam Shittu ne saboda siyasa. Ya yi barazanar za su fasa kwai mai wari in an kai su bango.

Wani rikicin da Shugaban ke fuskanta shi ne na wasu da ke neman yin takarar Gwamna a Jihar Katsina.

Duk neman wannan kujerar suna zargin Malam Shittu ya karkata ne ga Alhaji Mustafa Inuwa, Sakataren gwamnatin Katsina.

’Yan Majalisar Jiha ma suna da nasu korafin na cewa, tunda suka hau kan kujerunsu shekaru biyu da doriya, jam’iyya ba ta taba kiran su ba don taro, ko kuma ta saurari mene ne matsalolinsu?

Wani sabon rikici da ke ruruwa shi ne na kwangila da ake cewa gwamnatin Jiha ta bayar don a siyar a raba wa ’yan jam’iyya ribar da aka samu.

Ana ta yawo da kiyasin kudin kwangilar a farashi daban-daban da kuma abin da ya kamata a bai wa ’yan jam’iyya da yadda za su raba a tsakaninsu. Maganganun sun yi sama, kuma suna ta yawo da zama abin tattaunawa, amma uwar jam’iyya ta yi gum da bakinta.

Wannan ya kai ga wasu har sun fara kira ga gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya sa baki.

Katsina City News

www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here