Daga Bilya Hamza Dass

Al’amarin wanda ya faru da safiyar Asabat, a wani ƙauye me suna Tera na Tillabery dake kudancin ƙasar. Wani shaida da ya dayaga farkon faruwar lamarin ya shaidawa manema labarai cewa; “Mutane dayawa suka fito bayan anji labarin cewa, sojojin ƙasar Faransa zasu biyo ta hanyar su wuce zuwa wani babban sansani da suka tanada domin atisaye da kuma matsugunnin su a kusa da garin nan, sai mutane suka tare su suna ƙoƙarin hana su wucewa” Inji shi

Ya ƙara da cewa; da farko sojojin sun dinga duka da abubuwan hannun su kafin suka fara jefa Tiyagas, da kuma harbi da harsashi wanda ya tilasta mutane suka watse” ya ƙara da hakan. An cigaba da kai ruwa tsakanin jami’an tsaron da mutanan gari a kauyen Tera cikin jahar Tillabery, dalilin tsarewar da mutane suka ma sojojin Faransa.

Wani me suna Bachir Moutari da aka yaɗa saƙon Bidiyon shi yana martani kan lamarin yace tawagar wacce ta taso daga Bulkina sun harbi mutane da dama a kauyen Tera, inda ya zargi Sojojin ƙasar da bawa tawagar Sojojin goyon baya. Har yanzu ba’a gama tantance adadin mutanen da aka harba ko aka kama sanadin rikicin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here