RIJIYAR UWAR YA YA A GARIN BATAGARAWA

Daga Lawal Yahaya kofar bai

Wannan itace sananniyar Rijiyar da ake kira Rijiyar Uwar ‘ƴaƴa a kudancin garin Ɓatagarawa.
An gina ta shekaru aru aru.
Dalilin da ya sa ake ce mata uwar-ƴaƴa shi ne a zamanin da rijiyar take ganiyarta, akwai wadanda suka yi imanin cewa duk matar da ake tsammanin ba ta haihuwa ko kuma ta daɗe ba ta haifu ba, idan ta sha ruwan rijiyar za ta haifu. Mata da yawa da ke cikin garin Ɓatagarawa da kewaye sukan zo su sha ruwan wasu kuma a diba a kai masu don su samu haifuwa. Akwai kuma wata sananniyar rijiya da ake kira rafin-waje daga arewacin Ɓatagarawa.
( Lawal Yahaya K/ bai 1998.)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here