Home Sashen Hausa Rediyo faransa ya wallafa labarin mutuwar sarauniyar Ingila da wasu fitattun mutane...

Rediyo faransa ya wallafa labarin mutuwar sarauniyar Ingila da wasu fitattun mutane 100 a duniya

RFI ta wallafa labarin mutuwar Sarauniyar Ingila

Sarauniyar Ingila

Gidan rediyon Faransa RFI ya nemi gafara kan labaran ƙarya da ya ƴada na mutuwar shahararrun mutane kusan 100, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta Ingila da kuma fitaccen ɗan ƙwallon Brazil Pele.

Radio France International da ke yaɗa labarai a harsuna da dama ya wallafa labaran mutuwar ne a shafin Intanet.

Amma kafar ta ce matsalar na’ura ce ta sa aka wallafa labaran mutuwar fitattun mutanen.

Sauran waɗanda RFI ta wallafa cewa sun mutu, sun haɗa da tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter da Raul Castro na Cuba da kuma jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei.

Yawanci dai kafafen ƴada labarai kan tattara tare da shirya labaran mutuwar fitattun mutane domin wallafa su nan take lokacin da aka sanar da mutum ya mutu.

Kafar ta ce labarai sama da 100 aka wallafa kan kuskure kuma ba a shafin RFI kawai ba har da na abokan hulɗa da suka haɗa da Google da Yahoo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Meat, Tomatoes And Onions Prices Triple As Food Scarcity Looms In Awka

Meat, Tomatoes And Onions Prices Triple As Food Scarcity Looms In Awka By Emmanuel Okonkwo (ABS Reporter) Residents and fresh food dealers in Awka and its...

We brought in Fulani from Mali, Sierra Leone, Senegal, others to win 2015 election, after election, they refused to leave — Kawu Baraje

We brought in Fulani from Mali, Sierra Leone, Senegal, others to win 2015 election, after election, they refused to leave — Kawu Baraje Abubakar Kawu...

THE WHISTLER INVESTIGATION: Banditry In Nigeria: How Security Agencies Aid Illegal Arms Supply (Part 1)

THE WHISTLER INVESTIGATION: Banditry In Nigeria: How Security Agencies Aid Illegal Arms Supply (Part 1) By Tajudeen Suleiman On Mar 3, 2021 Shehu-Rekep-deputy-of-an-armed-group-of-bandits-in-Nigerias-northwestern-Zamfara-state.j Shehu Rekep, deputy of...

‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Uku Da Rana Tsaka A Katsina

'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Uku Da Rana Tsaka A Katsina Da misalin karfe ukku na ranar yau Talata, 'Yan bindiga dauke da bindigogi sun...
%d bloggers like this: