‘Yan Bindiga sun shiga wani sashe na barikin Sojoji dake Jaji Jihar Kaduna inda suka saci shanun sojojin suka yi awon gaba dasu.

Sun shiga wajan ne da misalin karfe 2 na daren ranar Alhamis inda suka yi harbi a Iska kamin suka sace shanun, kamar yanda Sahara Reports ta ruwaito.

Ba’a dai san yawan shanun da ‘yan Bindigar suka dauka ba amma wani shaida ya bayyanawa Sahara Reports cewa akalla shanun zasu iya kai 100.

Majiyar dai ta kara da cewa, a shekarar data gabata ma saida ‘yan Bindigar suka shiga suka sace shanu kusan 400 mallakin sojojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here