Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya Ta Yi Silar Zubar Da Hawayen Aminu Dantata Yayin Gudanar Da Taro

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata da ke jihar Kano a Arewacin Najeriya, ya zubar da hawaye akan yadda matsalolin tsaro su ka yiwa yankin Arewacin ƙasar dabaibayi.

Aminu ya zubar da hawayen ne a gurin bikin ƙaddamar da littafin Tabswiratul Hukkam da aka gudanar a babban ɗakin taro na jami’ar Bayero a jiya Asabar.

Hamshaƙin attajirin ya ce a halin da ake ciki yanzu yan Najeriya ba su da kwanciyar hankali akan dukiya da rayuwarsu a lokacin da su ke tafiye-tafiye ko kuma ma a gidajen su.

Tun da farko, Alhaji Aminu shi ne ya ɗauki nauyin fassara da buga littafin na Tabswiratul Hukkam, wanda ya ke jawabi akan shari’ar Muslunci, kuma wannan littafi zai zamewa alkalai jagora a lokacin gudanar da shari’o’i a kotuna.

Hare-haren yan fashin daji da satar mutane domin karbar kudin fansa na daga cikin manyan matsalolin da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi.

Taron kaddamar da littafin ya samu halarcin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here