Yayin da Nijeriya, musamman ɓangaren arewacin ƙasar ke fama da rashin tsaro, wanda ƙungiyoyin ƴan ta’adda ke addabar wasu sassa na yankin, an umarci limaman masallatan Juma’a da su shirya huɗaubar su ta gobe juma’a a kan zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa Shugaban Majalisar Limaman Masallatan Juma’a na Jihar Kano, Sheikh Muhammad Nasir Adam ne ya bada umarnin yayin ganawarsa da manema labarai.

Sheikh Muhammad Nasir, wanda shine Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Isyaka Rabi’u da ke Ƙofar Mata, ya ce zaman lafiya shi ne ƙashin bayan cigaban kowace al’umma, inda ya ce ” don haka na baiwa Limaman Jihar Kano Umarnin yin huɗuba akan hakan.”

“Addinin Musulci ya baiwa Zaman Lafiya muhimmanci sosai ,shi yasa ake Kiran addinin a matsayin addinin zaman lafiya, don haka mu ka bada umarnin ga limamai dau yi amfani da damar da Allah ya basu Wajen fadakar da al’umma muhimmancin zaman lafiya” inji Sheikh Nasir Adam.

Sheikh Adam ya ƙara da cewa suma limaman masallatan unguwanni na Khamsussalawatu da ke faɗin jihar nan su cigaba da Addu’o’in Samun zaman lafiya a jihar kano da kasa baki daya.

Shehun Malamin yayi fatan samun sauƙi ga sauran jahohi da ƙasashen da iftila’in rikici ya addabe su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here