A makarantar sakandaren koyar da fasaha dake Bukuru ‘Government Technical College Bukuru (BUTECHS)’ dake jihar Filato ne wani dalibi ya kashe malaminsa saboda malamin ya ladabtar da shi kan wani laifi da ya yi.

Dalibin mai suna Odeh wanda aka fi sani da ‘Romeo’ ya kashe malaminsa mai suna Job Dashen a karshen makon jiya.

Marigayin ya hukunta dalibinsa Dashen saboda bai zo dakin cin abinci da wuri ba wanda yin hakan karya dokar makaranta ne.

A dalilin haka Dashen ya hukuntashi ta hanyar yi masa bulala bisa ga sharadun makarantar.

Bayan ya yi masa bulala ne Odeh cikin fushi ya ruga dakin kwanan su ya suntumo wuka da yake boye da ita a gefen gadon sa ya nufi malamin ya caka masa.

Bayan caka masa da yayi, sai ana dauki Dashe ranga-ranga zuwa asibiti amma kuma sarar da yayi masa da wannan wuke ta riga ta yi wa Dashe Illa, ya rasu a asibitin.

Ganin haka kuwa sai Odeh gudu, amma kuma cikin dan kankanin lokaci jami’an tsaro suka kama shi bayan kama abokan sa da suka yi.

Mahaifiyar Odeh a yayin da ta je yi wa iyalan Dashen ta’aziya ta bayyana cewa ba yanzu ba take zargin Odeh ya shiga kungiyar Asiri saboda irin dabi’un sa da take gani.

Dashen ya rasu ya bar matarsa da tsohon cikin ta na faru.

Rashin isasshen tarbiya da iyaye basu bai wa ya’yan su musamman iyayen zamani ya sa ake samun kangararrun yara.

Mafi yawan iyaye a wannan zamani basa kwaban ‘ya’yan su koda sun ga yaran na aikata abin da ba daidai ba.

Hanyar da shine mafita ga al’umma shine iyaye su rika maida hankali wajen baiwa yayan su tarbiyya nagari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here