Mai bawa Gwamnan Katsina Shawara akan sha’anin tsaro, Malam Ahamad Katsina

Rashin hukunci na daya daga cikin abinda ya ta’azzara matsalar tsaron da muke fama da ita a Jihar Katsina. “Inji Mai Martaba Sarkin Katsina.

Rahoton Surajo ‘Yandaki

Mai Martaba Sarkin Dr. Abdulmuminu Kabir Usman ya fadi hakan ne”, ranar Alhamis 14/10/2021, a wani taro na musamman na hadin gwiwa da aka gudanar, a cikin kokarin da ake na nemo hanyoyin kawo karshen matsalar tsaron da Jihar Katsina take fama dashi.

Taron ya tattauna akan tsaiko da ake samu wajen tafiyar da harkokin Shari’ah a kotuna wajen hukunta masu laifi, mahalarta taron sun nuna rashin jin dadinsu akan yadda ake samun jinkiri wajen hukunta masu aikata Manyan laifuffuka musamman wadanda ake samu da aikata ayyukan ta’addanci a cikin Jihar Katsina.

Da yake gabatar da jawabinsa yayin gudanar da taron Mai Martaba Sarkin Katsina Dr. Abdulmuminu Kabir Usman ya bayyana cewa” rashin hukunci ga masu aikata ta’addanci na daya daga cikin abinda ya ta’azzara matsalar tsaron da muke fama da ita, samun hukunci cikin sauri zai taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a cikin Jihar nan.

Taron ya bada shawara guda biyu, na farko kodai a kirkiro da kotu ta musamman da zata rika hukunta masu aikata ta’addanci cikin sauri, ko kuma kotunan su canja salon yadda suke tafiyar da harkokin shari’unsu na yau da kullum ta yadda za a rika samun hukunci cikin sauri ga masu aikata ta’addanci a cikin Jihar nan.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Katsina

Taron da aka gudanar a Babban dakin taro na hukumar kula da Ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar Katsina ya samu halartar Mai baiwa Gwamna Shawara akan Harkokin tsaro Alh. Ibrahim Katsina, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alkalin Alkalai na jiha, Wakilin Babban Jojin Jiha, Kwamishinan ‘yan Sanda, Kwamishinan Shari’ah, Hakimai da Magaddai da sauran masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here