RASHIN DA’A: Masarautar Bauchi Ta Dakatar Da Wakilin Birni

Daga Khalid Idris Doya

Masarautar Bauchi ta dakatar da Hon. Yakubu Shehu Abdullahi daga Sarautar Wakilin Birnin Bauchi bisa zarginsa da rashin ladabi da biyayya wa Sarki da gwamnati.

Wannan dakatarwar na kunce ne ta cikin wasikar da Majalisar Sarkin Bauchi ta aike wa Hon. Shehu Abdullahi wanda muka ci karo da kwafinta dauke da sanya hannun Nasiru Musa Maidala, a madadin sakataren Majalisar Sarkin da ranar yau din nan.

Yakubu Shehu dai shine mambar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar cikin garin Bauchi, an dakatar da shi ne bisa zaman gaggawa da majalisar Sarkin ta gudanar a yau kuma ta amince da dakatar da shi bisa abun da suka kira ‘Raini ga Sarki’ da sarakuna hadi da gwamnati.

Majalisar Sarkin ta kuma buga misali da ababen da suka wakana jiya a gidan gwamnatin Bauchi yayin da sarakuna ke kai ziyarar gaisuwar sallah ga gwamnan Bauchi Bala Muhammad a gidan gwamnati.

“A zaman Majalisar Sarki na yau 16/5/2021 karkashin Mai Martaba Sarkin Bauchi, ta yi nazari mai zurfi kan irin abubuwan da kake yi wadanda raini ne ga Sarki, Shugabanni, ‘Yan Majalisan Sarki, Hakimai da Sarakuna; ta yi misali da yadda kake shiga kan Sarakuna da Alkyabba da Kandiri, kuma an yi maka gargadi a kai.

“Abun da ya faru jiya a wato ranar Asabar 15/5/2021 a gidan gwamnatin jihar Bauchi ya nuna ka raina Sarki, Masarauta, Gwamna, da Gwamnati kuma Majalisa ba za ta yarda da wannan ba.

“Saboda haka ta dakatar da kai daga matsayin Sautar Wakilin Birnin Bauchi har sai abun da hali ya yi.”

Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin Wakilin Birnin abun ya ciruta zuwa hada wannan rahoton domin wakilinmu ya kirashi tare da aike masa da sakon kar ta kwana amma dukka babu amsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here