Home Sashen Hausa Ranar Talata za a ƙaddamar da shirin ɗaukar 'yan Najeriya 774,000 aiki

Ranar Talata za a ƙaddamar da shirin ɗaukar ‘yan Najeriya 774,000 aiki

Ranar Talata za a ƙaddamar da shirin ɗaukar ‘yan Najeriya 774,000 aiki

Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ƙaddamar da shirin ɗaukar mutum 774,000 ɗauki a faɗin ƙasar.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya sahale ƙaddamar da shirin Special Public Works na ɗaukar ‘yan Najeriya marasa aikin yi guda 774,000 aiki,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa “za a fara aikin ne daga gobe Talata, 5 ga Janairun 2020. Duka ofisoshin hukumar ɗaukar aiki (NDE) na jihohi sun shirya tsaf domin fara shirin.”

Gwamnati ta tsara ɗaukar mutum 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma 774 na ƙasar domin rage yawan matasa marasa aikin yi a ƙasar.

An sha ce-ce-ku-ce tsakanin Mista Keyamo da ‘yan Majalisar Wakilan Najeriya game da wanda ya kamata ya aiwatar da shirin, inda suke neman a ba su wani kaso na mutanen da za a ɗauka.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zamfara: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Makarantar Jangebe Sun Bi Sawun Yaransu Cikin Daji

Zamfara: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Makarantar Jangebe Sun Bi Sawun Yaransu Cikin Daji Iyaye da kuma 'yan uwan ɗaliban da aka sace a...

Iyalan Ɗaliban da suka rage, suna kwashe ‘ya’yansu daga makaranta a Zamfara

Iyayen daliban da suka rage suna kwashe 'ya'yansu daga makarantar da aka sace dalibai mata fiye da '300' a jihar Zamfara.

‘Yanbindiga sun sace daliban makaranta a Jihar Zamfara

GGSS Jangebe: Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 a jihar Zamfara Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar...

Kakakin Majalisar Dokoki na jihar katsina ya amshi bakuncin Kwamitin shiga tsakani don wanzar da zama lafiya

Da yammacin yau Alhamis 25/02/2021 Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi'u Musa Maigari Zango ya amshi bakuncin Tawagar Kwamitin shirin shiga...

Kotu ta ci tarar kakakin ’yan sandan Kano miliyan daya

Kotu ta ci tarar kakakin ’yan sandan Kano miliyan daya Rigar'yanci Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ci tarar kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP...
%d bloggers like this: