Ranar Qudus Ta Duniya; Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Gudanar Da Jerin Gwanon Bai-Daya A Jihohin Nijeriya.

Daga A.I Musa.

Sanannnen al’amari ne cewa, duk juma’ar karshen watan Ramadan, Musulmi a fadin duniya musamman mabiya Mazhabar Shi’a, kan gudanar da jerin gwanon Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa sakamakon shelar yin hakan da Imam Ruhollah Al-khomaini na Iran ya yi a shekarar 1979.

A Najeriya, Mabiya Mazhabin na Shi’a, ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Al-zakzaky kan bi sahun al’ummar Musulmi wajen gudanar da wannan jerin gwanon duk shekara, inda a bana ma suka gudanar da shi a ranar juma’ar nan 25 ga Mayu, 2021.

A lokacin gudanar da jerin gwanon Muzaharorin, sun fito kwansu da kwalkwata inda suka hau kan tituna dauke da Hotunan Palasdinawa masu nuna yadda Isra’ila ke muzgunawa Palasdinawan ta hanyar rusa masu gidaje da jefa masu nakiyoyi har ma da Bama-bama da kuma yi masu kisan gilla ba tare da rarrabe Yaara da Mata ko Manya da Tsofaffi.

Hakazalika, ‘yan shi’ar sun hau kwalta tare da daga hotunan shugabansu Shaikh Ibraheem Alzakzaky, dauke da rubutu kala-kala masu yin kira da cewa a sake shi.

Har wayau, ‘yan uwa Musulmin suna tafiya tare da rera wakoki alhini a kan abin da Isra’ila ke yi wa Pasdinawan, sannan kuma rera wakokin neman a saki Malamin nasu da Matarsa Malama zeenatu Ibraheem, wadanda suka shafe kusan tsawon kusan shekaru Bakwai a tsare.

Garuruwan da aka gudanar da jerin gwanon Muzaharorin dai a bana sun hada da: Babban birnin tarayya Abuja, Kaduna, Zariya, Kano, Katsina, Daura, Malumfashi, Sokoto, Bauchi, Gwambe, Talata Mafara da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here