Advert
Home Sashen Hausa Ranar lahira ba mu kaɗai za'azo damu ɗaɗɗaure ba, hada 'yan Social...

Ranar lahira ba mu kaɗai za’azo damu ɗaɗɗaure ba, hada ‘yan Social media da ƴan jarida, Amma mu shuwagabanni adalcin mu ne zai fidda mu- Gwamnan katsina, Aminu Bello Masari

Ofishin Mai baiwa Gwamnan Katsina shawara akan harkokin tsaro hadin gwiwa da Kungiyar yan Jarida ta kasa reshen jihar Katsina, sun gudanar da taron kara ma juna sani.

 

Taron ya gudana ne ga ‘Yan Jarida, ma’aikatan sashen yada labarai na kananan hukumomi, da masu amfani da kafar sadarwar zamani (Social Media),

Anyi taron ne akan yadda za’a inganta harkar tsaro bisa kwarewa ta aikin Jarida a.

An gudanar da taron kara ma juna sanin a Babban Dakin taro na Hukumar kula da Ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar Katsina dake bisa hanyar zuwa Kaita nan cikin Garin Katsina.

Taron ya samu Halartar Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, da kwamishinan yaɗa labarai na jiha Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika.

A cikin jawabin sa Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, Ba Shugabanni kadai za’a zo da su daure ba ranar gobe kiyama, harda yan jarida da yan ‘social media’ masu rubuta labarin ƙanzon kurige da yaɗa sharri, domin haddasa fitina a cikin al’umma, “mu kuma shuwagabanni Adalcin mu ne zai kwance mu”

Haka zalika ya yi kira ga malamai da suji tsoron Allah kada su maida mimbarin su wajen yaɗa maganganun da basu da masaniya akan su.

“Naso a wannan taron ace an gayyato malamai domin suma suna da gudumawar da suke badawa, saboda dayawa daga cikinsu sun ɗauka cewa wan’nan mimbari na firi huɗuba wata hujja ce ta bada labarin abinda baka da ilimi akanshi.

Mutum zai zo yana gayamaka wani abinda ya shafi Gwamnati amma ko kansila bai taba zantawa dashi ba, ya haƙiƙance akan abinda bai da tabbas akanshi, mutimin da za’ai magana kanshi,ba ai mashi uzuri ba, ba’a kirashi an zanta dashi ba, a’a kawai wan’nan jin, da yayi na waiwai, shine zai zama makami na bada hujja akanshi.” Inji Gwamna Masari.

Kwararrin Malamai Masana a fagen aikin Jarida da kafar sadarwar zamani ‘Social Media’ suka gabatar da kasidu a wurin taron kara ma juna sanin, Wanda suka hada da!

1.  Dr Mukhtar El-kasim (PhD) Malami a Sashen koyar da aikin Jarida na makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, ‘Hassan Usman Katsina Polytechnic’.

2. Dr. Samaila Balarabe shima Malami a sashen koyar da aikin Jarida a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, ‘Hassan Usman Katsina Polytechnic’.

3. Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan ilmi Mai Zurfi.

3- Malam Samu Adamu Bakori Babban Limamin Masallacin Juma’a na Bani Kumasi dake nan cikin Garin Katsina.

Sauran mahalarta taron sun hada da, Mataimakin Gwamna jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, Wakilin kakakin majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba Dan majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Katsina, Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin tsaro Alh. Ibrahim Ahamd Katsina, Wakilin Sarkin Katsina dana Daura, da Sauran ƴan jaridu na ciki da wajen jihar ta katsina.

Anbi dokoki da ƙa’idojin da hukumar NCDC ta sharɗanta yanda ya kamata domin kaucewa yaɗuwar cutar mashaƙo (COVID-19)

Katsina City News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: