RAN MAZA YA BACI: Bafarawa Zai Shige Gaba Wajen Kwatowa ‘Yan Arewa Hakkinsu Na Asara Da Sukayi Lokacin Zanga-zangar EndSars
Tsohon gwamnan jahar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce ya na jagorantar tattara bayanan asarar rayuka da dukiya da al’ummar arewa su ka yi don mikawa ga majalisa ko gwamnatin taraiya na neman diyyar da ta kai Naira tiriliyan 7.
Wannan ya biyo bayan matsayar da kakakain majalisar wakilai Femi Gbajabiamiala ya dauka na kauracewa sanya hannu kan kasafin kudin badi Sai gwamnati ta biya diyya ga wadanda cin zarafin ‘yan sandan SARS da aka rushe ya shafa.
In za a tuna Gbajabiamiala a jawabi gaban zauren majalisar ya ce ba zai sa hannu kan kasafin kudin 2021 ba sai ya kunshi diyya ga wadanda cin zarafin ‘yan sanda a shekaru goma da su ka wuce.
Wannan dalili yasa muma muka nemi a biyamu diyyar mutanen mu na Arewa da suka tafka asara lokacin wannan zanga-zanga wadda takai ga rushe rundunar SARS tareda juyawa zuwa bangaranci tareda lalata dukiyar ‘yan Arewa. Inji Bafarawa.