Rahoton musamman
‘YAN BATSARI DA AKAYI GARKUWA DASU..SUN HAURA KWANAKI HAMSIN …..

Daga Misbahu Ahmad Batsari
@ jaridar taskar labarai

Ranar laraba 07-07-2021 mutanen Batsari suka cika kwanaki hamsin (50), a hannun masu garkuwa da mutane.

Idan ba a manta ba tun ranar talata 18-05-2021 ‘yan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka afka cikin garin Batsari ta jihar Katsina, inda suka yi harbe-harbe tamkar a fagen fama, suka bindige wani dattijo wanda nan take yace ga garinku nan, sannan suka kama mutane ashirin da takwas (28), wadanda galibinsu mata ne da kanana yara, ciki harda yara marassa lafiya, suka yi awon gaba da su har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

A tattaunawar mu da iyalan wadanda abin ya shafa sun bayyana mana irin halin da suke ciki na takaici da bakin ciki, abin baya misaltuwa.

Sun koka kwarai da gaske ganin yadda aka yi shiru da maganar kamar su ba ‘yan Batsari bane? Ko su gwamnati bata da bukatar su?

Da yawansu sun kare jawabansu da kuka, dalili kenan da yasa na katse hirar, na taya su addu’ar Allah ya kubutar dasu cikin aminci.

Ga jerin sunaye wadanda ke hannunsu;
1. Marwa Bello.
2. Zainab Bello.
3. Muhammad Bello.
4. Yakubu Bello.
5. Rabi Bello.
6. Sahura Haruna.
7. Zaharaddeen Haruna.
8. Rabi Amadu.
9. Nafisa Amadu.
10. Rabi Ibrahim.
11. Mufida Ibrahim.
12. Yusuf Ibrahim.
13. Rabe Mannir.
14. Anasiyya Ado.
15. Saliha Ado.
16. Habibu Ado.
17. Ta-mama Kurma.
18. Khadija Dayyabu.
19. Fatima Dayyabu.
20. Hadiza Saidu.
21. Rahima Abdulkadir.
22. Aminu Umar.
23. Nusaiba Umar.
24. Mujahid Umar.
25. Samaila Umar.
26. Hussaina Umar.
27. Al-ameen Umar.
28. Sadiq Amadu.

Da yawan jama’a na mamakin yadda al’umma suka yi shiru da lamarin wadannan bayin Allah, har ma wasu na cewa ko don su ba kowa bane ko kuwa don abin bai taba gidajen manyan garin ba?

Ina ‘yan siyasar garin suke zababbu, masu rike da manyan mukamai a gwamnati, mi kukeyi domin ceto rayuwar wadannan bayin Allah?
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777246
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here