Advert
Home Sashen Hausa RAHOTON MUSAMMAN; YADDA AKA FID DA SABON SHUGABAN APC A JAHAR...

RAHOTON MUSAMMAN; YADDA AKA FID DA SABON SHUGABAN APC A JAHAR KATSINA

Muazu Hassan  @Karsina City News

A ranar Laraba 13 wajen wani taron wasu bangaren masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, ba wanda ya san mene ne ajandar taron.

Gwamnan Katsina shi ne ya fara magana cikin damuwa da bacin rai, inda ya bayyana yadda jam’iyyar APC ta taho da tsarin fid da ‘yan takara a mukaman siyasa, amma wasu masu neman Gwamna suna ta bata masu shiri.

Mutune biyu da ke dakin taron sun tabbatar mana Gwamnan har sunaye ya kama.

Daga nan ya ce to ga maganar zaben shugabannin jam’iyya na Jiha ta zo, ya za a yi?

Wanda ya fara magana kamar yadda majiyoyi biyu suka tabbatar da magana daya shi ne, Sakataren gwamnatin Katsina, Mustafa Inuwa, ya fara da cewa shi ba wanda ya taba fada wa yana neman Gwamna. Ya yi dogon bayani na kare kansa.

Wanda ya yi magana ta biyu shi ne mataimakin Gwamnan Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, shi ma ya kare kansa.

Majiyarmu ta ce ya yi magana mai tsawo, wadda bai taba irinta ba a wani taro a baya.

Daga nan sai aka yi ta sanya albarkcin baki. Wannan ya fada, wannan ya mayar.

Duk taron an jinjina wa Gwamnan Katsina a kan yadda ya kyale aka yi zabubbakan unguwani da Kananan Hukumomi ba tare da katsaladan ba.

Har aka zo kan Dakta Rabe Nasir, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha a matsayinsa na mai Digirin digirgir, kuma tsohon jami’in tsaron farin kaya shi ne ya canza alkiblar zaman.

A jawabinsa ya fito da sanka-sankar abin da Gwamna ke magana, kuma abin da yake tsammanin taron zai ba da amsa.

Ya kawo duk ‘yan takarar da ake jin suna nema, da wadanda ake jin suna son dama ta samu su fito.

Ya ce; “Amma mu koma tsarin mulki da tsare-tsaren jam’iyyar APC ta Kasa” .

Rabe Nasir ya nemi Kwamishinan Shari’a ya yi bayani.

Kwamishinan Shari’a, Barista Ahmad Elmarzuk, ya buda tsarin mulkin jam’iyyar APC, ya karanto duk bayanan kowane.

Da Kwamishinan Shari’a ya gama, Rabe Nasir ya yi karin haske. Sai ya ce kun ji inda muke a yanzu.

Majiyarmu ta ce a nan ne, wuta ta dauke wa kowa a dakin taron, a lokacin duk wani motsi sai kowa ya ji.

“Muka zama kamar wadanda ruwa ya ci. Gwamnan yana kallon kowa yana sunkuyar da kai kasa. Kana iya jin lumfashin na kusa da kai saboda tsit”, in ji mai ba mu labari.

Can sai Gwamnan ya ce ga mafita. Sakataren jam’iyya ya zama Shugaba, Shittu S. Shittu ya zama Sakatare, Bala Abu Musawa kuma, ya zama mataimakin Shugaba na Jiha. Sauran mukaman kuma a raba su a tsakanin Kananan Hukumomi, kowace Karamar Hukuma ta kawo wanda zai yi mata.

Ya ce a je a sulhunta da tattaunawa. A kan haka aka tashi taron.

Jaridun Katsina City News sun samu labarin wa aka ba jam’iyyar tun fitowa taron, amma sai da suka dau awa daya suka tabbatar daga majiyoyi guda, sannan suka fara sakin labarin.

Shafin watsa labarai na Katsina City News suka fara fasa labarin, daga nan ya yadu kamar wutar daji.

SABON SHUGABAN APC
Tun bayan saka ranar zaben sabon Shugaban ke shigi-da-fici yana rokon alfarma kar a bar shi a kasa, a samu wata kujera a makala masa.

Bai taba kawo wa ransa zai zama Shugaba ba.

A Sallar Asubar ranar Laraba, wani dan’uwansa ya roki a karanta masa Suratul Ikhlas kafa uku da nufin Allah ya sanya a ba shi mataimakin Shugaban jam’iyya na shiyyar Daura.

“Duk addu’arsa da biyayyarsa da kamun kafa, kar a ba shi a kasa ba wani mukami ko ya yake”, in ji wani Abokinsa.

Hatta ranar da aka yi taron masu ruwa da tsaki da ka gan shi ka san ji yake kamar mafarki yake, kamar yadda babban Editan jaridun Katsina City news ya lura da shi.

ALBARKAR MAHAIFA CE
Wani da ya san shi, ya san iyayensa, ya ce, wannan daukaka da ta same shi kwatsam bai shirya ba, bai kuma tsammani ba, ba ta rasa nasaba da albarkar Mahaifa.

Ya ce Mahaifinsa jami’in Ma’aikatar Ilmi ne. Ya taimaki mutane lokacin yana da rai. Zai dauke ka aikin malanta, ya kuma tura ka karatu, kana aiki kana yi.

Babansa ya taimaki mutane, kuma ana yi wa zuriyarsa addu’a.

Bai nema ba, kuma ba wata kulla-kullan siyasa ba ce, Allah ya ba shi.

Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...