Ana hasashen sama da Mutum Hamsin ne suka Mutu a garin na Kwandago, Inda masu hakar Zinari suke…

Wani yanki da ake dibar Zinari a wajen

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Tun bayan da aka gano akwai Zinari a kauyen Kwandago dake karamar hukumar Dan’Issa a Jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar mutane ke tururuwa, daga ko ina a Arewacin Najeriya da Nijar suna ɗibar rabon su, inda masu hannu da shuni suke bin mahakan, idan suka samu, sukuma sai su saye Zinari, a wani bincike da Katsina Post tayi a watan da ya shude angano ‘yan asalin jihar katsina sama da mutum dubu goma suke hakar zinari a wajen. Katsina City News ta zanta da wani da yake kai kayan masarufi domin sayarwa, inda ya bayyana mana cewa rayuwa tayi tsada, inda ake saida Jarkar ruwa akan Naira 250

Shin ko Gwamnati da hukumomin yankin zasu iya daukar wani mataki, duba da yanda aka fara samun asarar rayuka a wajen… ?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here