Advert
Home Sashen Hausa Rahama Sadau da Maryam Sanda na cikin mutanen da suka fi tashe...

Rahama Sadau da Maryam Sanda na cikin mutanen da suka fi tashe a intanet a Najeriya a 2020-BBC hausa

Rahama Sadau da Maryam Sanda na cikin mutanen da suka fi tashe a intanet a Najeriya a 2020

Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa ta Kannywood Rahama Sadau ce mutum ta huɗu da ta fi tashe a intanet a shekarar 2020 a Najeriya.

Sannan kuma Rahaman ta shiga jerin mutanen da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google a shekarar 2020 a Najeriya, inda ta zo ta tara daga cikin mutum 10.

Kazalika a bayanin da shafin Goggle ɗin ya fitar Maryam Sanda ita ce mutum ta tara cikin goman da suka fi tashe a bana a intanet a Najeriyar.

Shafin Google yakan fitar da kalmomi ko kuma sunayen da mutane suka fi bincikawa a shafin duk shekara a kowace kasa a fadin duniya.

Sannan kuma shafin kan yi wa sunayen rukuni ne, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da ‘yan fim da fina-finan kansu da kuma tambayoyi.

Ga alama dai Rahama Sadau ta shiga wannan jeri ne sakamakon wani abu da ya faru da ita a watan Nuwamban 2020 ɗin, inda aka samu hatsaniya a intanet bayan ta wallafa wasu hotuna tsakanin masu goya mata baya da masu sukarta.

Hotunan da ta wallafa ɗin sun jawo har wasu suka yi saɓo na kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu, abin da ya jawo babban tashin hankali.

Ita kuwa Maryam Sanda matar da ake zargi da kashe mijinta a 2017, ta shiga jerin ne bayan da a farkon shekarar nan wato a watan Janairu wata Babbar Kotu a Abuja ta zartar mata da hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayanan bidiyo,Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

Maryam ta ɗaukaka ƙara a watan Fabrairu sai dai a watan Disamba Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta tabbatar da hukuncin kisan.

Wataƙila faruwar waɗannan al’amura uku a cikin shkearar ne suka sa Maryam ta zamo cikin waɗanda suka yi tashe a intanet ɗin a Najeriya.

Kazalika, fitacciyar ƴar gwagwarmayar nan Aishatu Yesufu ce ta tara a jerin rukunin tambayoyin da aka fi yi a shafin Goggle a 2020 a NAjeriya.

Aishatu wacce tun 2014 aka san ta da fafutukar ganin an ceto ƴan matan makarantar sakandaren Chibok, ta sake haskawa ne bayan da a watan Oktoba ta shiga cikin zanga-zangar kawo ƙarshen rundunar musamman ta ƴan sanda da ke yaƙi da fashi da makami wato EndSars a Abuja.

Wannan zai iya zama dalilin da ya sa aka dinga neman sanin wace ce ita a shafin Google.

Shi ma zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya fito a jerin rukuni daban-daban har uku, na mutanen da suka fi tashe a intenet da waɗanda aka fi neman ƙarin bayani a kansu a Google da kuma rukunin tambayoyin da aka fi yi a Google ɗin.

Bayanan bidiyo,Bidiyon Aisha Yesufu; Matar da ke zanga-zangar SARS sanye da hijabi

Jerin mutanen da suka fi tashe a intenet a Najeriya a 2020

1. Joe Biden

2. Rema

3. Naira Marley

4. Rahama Sadau

5. Hushpuppi

6. Laycon

7. Kamala Harris

8. Omah Lay

9. Maryam Sanda

10. Kai Havertz

Kamala Harris
Bayanan hoto,Mataimakiyar zaɓaɓɓen shugaban Amurka Kamala Harris ta fito a rukunin mutanen da suka fi tashe a intenet a Najeriya a 2020

Kalmomi 10 da aka fi neman ƙarin bayani a kansu a Google a 2020 a Najeriya

1. Coronavirus

2. US election

3. Joe Biden

4. Google Classroom

5. ASUU

6. Zoom Live

7. Rema

8. Naira Marley

9. Rahama Sadua

10. Hushpuppi

Joe Biden
Bayanan hoto,Shi ma zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana a rukuni uku da rukunan da aka fitar

Ko a shekarar 2019 ma tauraruwar fina-finan Hausa Hadiza Aliyu Gabon ta shiga cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google a Najeriya.

A lokacin ita ma Hadizar ta zamo ta huɗu a jerin na bara baya ga taurarin fim din kudancin Najeriya wato Nollywood, Regina Daniels da Genevieve Nnaji da Tonto Dike, da suke kan gaba.

Wannan layi ne

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Wace ce Aisha Yesufu? Tambayoyin da aka fi yi a shafin Google a 2020 a Najeriya

1. Who is the new President of America? – Wane ne sabon shugaban Amurka?

2. When is school resuming in Nigeria? – Yaushe za a koma makaranta a Najeriya?

3. How to make hand sanitizer – Ta yaya ake haɗa man goge hannu na sanitizer?

4. Who is George Floyd? – Wane ne George Floyd?

5. How to make face mask – Ta yaya ake ɗinka takunkumi

6. Who is Joe Biden? – Wane ne Joe Biden?

7. Who is Laycon? – Wane ne Laycon?

8. How to make cake – Yaya ake yin ket

9. Who is Aisha Yesufu? Wace ce Aisha Yesufu?

10. How to make bread – Yaya ake yin burodi?

Aishatu Yesufu

Waƙoƙin da suka fi tashe a 2020 a Najeriya

1. Davido – Fem

2. Simi – Duduke

3. XXXTentacion – Bad

4. Betty – Butter

5. Rema- Ginger me

6. Rema – Woman

7. Burna Boy – Wonderful

8. Patoranking – Abule

9. Naira Marley – Tesumole

10. Davido ft Nicki Minaj – Holy Ground

Abincin da aka fi neman ƙarin bayani kan yadda ake yin su a Najeriya a 2020

1. Pornstar martini recipe – Yadda ake Pornstar martini

2. Puff puff recipe – Yadda ake fanke

3. Pancake recipe – Yadda ake fanke

4. Red velvet cake recipe – Yadda ake ket me jar kala

5. Meat pie recipe – Yadda ake fanke mit fayif

6. Chin chin recipe – Yadda ake cincin

7. Bread recipe – Yadda ake burodi

8. Chocolate cake recipe – Yadda ake ket

9. Oha soup recipe – Yadda ake miyar Oha

10. Egusi soup recipe – Yadda ake miyar Agushi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA ...A tabbatar Da An Yi Adalci *Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal @Katsina City News Ranar Asabar 2...

Sheikh Zakzaky Meets Families and Survivors of Zaria Massacre

Sheikh Zakzaky Meets Families and Survivors of Zaria Massacre Some families of the those killed by the military in Zaria in December, 2015 met with...

HOTUNA; Malam Ibrahim Zak zaky ya gana da iyalan wadanda suka rasa yan uwansu. Wani hoto da shafin jaridar Al mizan ya fitar ya...

HOTUNA; Malam Ibrahim Zak zaky ya gana da iyalan wadanda suka rasa yan uwansu. Wani hoto da shafin jaridar Al mizan ya fitar ya...

A FIVE DAY OLD BABY, FIVE NURSING MOTHERS AND OTHERS ESCAPED FROM BANDITS’ CAMP

A FIVE DAY OLD BABY, FIVE NURSING MOTHERS AND OTHERS ESCAPED FROM BANDITS' CAMP Hassan Male @Katsina City News Katsina State government has called on the...
%d bloggers like this: