Advert
Home RA’AYIN JARIDAR VANGUARD: Wahalar Da Shaikh Zakzaky ya sha

RA’AYIN JARIDAR VANGUARD: Wahalar Da Shaikh Zakzaky ya sha

Fassarar Ammar Rajab

Bayan shafe fiye da shekara biyar a hannun sojoji da sauran hukumomin tsaro, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, Sheikh Ibraheem Zakzaky da matarsa, Zeenatu, sun shaki iskar ‘yanci, bayan da Babbar kotun Kaduna ta wanke su tare da sakin su a hukuncin da Alkali kotun, mai shari’a Gideon Kurada ya yanke.

Ma’auratan sun fito a gurgunce, alama da ke nuni da wahalar da suka sha a yayin da suke hannun gwamnatin Muhammadu Buhari a tsawon fiye da shekaru biyar. Hakan ya biyo bayan kisan kiyashin da sojoji suka yi musu a yayin gabatar da taron su na shekara-shekara, bisa zargin ‘tarewa’ tsohon shugaban rundunar sojin Nijeriya, Tukur Burutai ‘hanya’, wanda hakan ya sanya sojojin suka je har gidan Shaikh Zakzaky daga ranar 12 zuwa 14 ga Disambar 2015, suka kashe mutum 347 da kuma bizne su a ramin bai daya.

An raunata daruruwan mutane. Shehin Malamin ya rasa ‘ya’yansa guda shida. Sojojin sun yi zargin cewa sun kai wa ‘yan shi’ar hari ne saboda sun nemi ‘kashe Burutai’. Shugaban kasa Buhari ya ce ‘yan Shi’ar ne suka takali sojoji da kansu. An kama Zakzaky a ranar 13 ga watan Disambar 2015, inda aka ci gaba da rike shi a hannun hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS har na tsawon shekara biyu da rabi duk da umurnin da kotu ta bayar a sake su. A ranar 15 ga watan Mayun 2018 aka sake gurfanar da su a gaban kotu.

Membobin Harkar Musulunci a Nijeriya sun gabatar da muzaharori ya fi a kirga a Kaduna da Abuja. Matsin da Zakzaky ya fuskanta ya yi iri daya da wanda tsohon mashawarci kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) ya fuskanta a hannun gwamnatin. Ci gaba da rike wa a hannun DSS ba tare da gurfanawar domin shari’a ba, rabon da a ga hakan tun zamanin mulkin soja, inda gwamnatin nan ta dawo da wannan salon ga wadanda take yi musu kallon makiyanta ne.

An ci zarafin tsarin mulkin da ya bayar da damar ‘yancin gudanar da rayuwa,’ yanci, shari’ar gaskiya da kuma mutunta Zakzaky da matarsa da membobin Harkar Musulunci. Wannan abin Allah-wadai ne kuma ba a bin yarda bane. Kundin tsarin mulkin mu ya bayar da umurnin gudanar da al’amuran kasarnan ne bisa tsarin mulki. Muna masu kira ga Zakzaky da Harkar Musulunci da su binciki dukkanin hanyoyin da tsarin mulki ya tanada domin neman biyan diyya bisa cin zarafin hakkokin su da aka yi.

Muna kuma yabawa Mai Shari’a Gideon Kurada bisa kiyaye martabar bangaren shari’a da ya yi a matsayin wuri ne na adalci ga ‘yan kasa marasa karfi a kan gwamnatin jihar dake da kayyadadden lokacin mulki. Gami da karawa, Harkar Musulunci da shugabancinta su koyi darasi daga abubuwan da suka faru masu ban tsoro da daga hankali domin gudanar da kansu cikin natsuwa a yayin gudanar da taron Arba’in na tattaki.

Halinsu na toshe hanyoyi da sanya tafiye-tafiye wahala ga sauran masu amfani da hanya ya kasance abin da mutane ke korafi akai. Nijeriya kasa ce da take da al’umma masu addinai da yawa.

Tsarin mulkinmu ya kuma bai wa kowa ‘yancin walwala. Dole ne mu girmama waɗannan don guje wa fushin ‘yan Nijeriya da kuma doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: