Raɗe-raɗin sauya sheƙa: Tinubu, Ganduje da Shettima sun ziyarci Goje

Wata tawaga mai karfi ta jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Jagoran Jam’iyar na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kai wa Sanata Danjuma Goje ziyara a gidansa da ke Asokoro a Abuja, a daren jiya Asabar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike; tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Philips Aduda kuma tsohon dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Billiri/Balanga na tarayya, Hon. Ali Isa JC su ka ziyarci Goje a Abuja inda su ka nemi ya koma PDP.

Tawagar ta Tinubu ta hada da gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima.

Ziyarar da shugabannin APC ɗin suka kai wa Goje ba za ta iya rasa nasaba da ziyarar da jiga-jigan PDP suka kai tun farko, wadanda suka je gidan Goje domin ganin sun dawo da shi jam’iyyarsa da ya bari tun 2014.

Idan dai za a iya tunawa, Goje wanda tsohon ministan wutar lantarki ne, wanda ya taba zama gwamnan jihar Gombe sau biyu, kuma a halin yanzu Sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, yana takun-saka da gwamna Inuwa Yahaya da kuma rikicin da ya kunno kai a cikin jam’iyyar APC, kuma mai yiwuwa a karshe ya yarda ya koma PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here