Advert
Home Sashen Hausa Prof. Muhamud Yakubu shugaban INEC ya miƙa ragamar shugabanci ga mai riƙon...

Prof. Muhamud Yakubu shugaban INEC ya miƙa ragamar shugabanci ga mai riƙon ƙwarya

Yakubu shugaban INEC ya miƙa ragamar shugabanci ga mai riƙon ƙwarya

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya miƙa ragamar mulkin hukumar ga Kwamishinan Ƙasa a hukumar, Air Vice Marshal (AVM) Ahmed Mu’azu (ritaya) kafin ya samu amincewar ci gaba da mulkin sa a karo na biyu.

A wani ƙwarya-ƙwaryan taron miƙa ragamar wanda aka yi a hedikwatar INEC a Abuja a ranar Litinin, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa bai dace a gare shi ya ci gaba da aiki ba daga ranar 9 ga watan Nuwamba, domin a ranar ne wa’adin sa ya ƙare, ba tare da Majalisar Dattawa ta tabbatar masa da wa’adin sa na biyu ba.

An rantsar da Yakubu da Kwamishinoni biyar ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2015, sannan aka rantsar da wasu Kwamishinoni shida a ranar 7 ga Disamba, 2016, da kuma ƙarin Kwamishina ɗaya a ranar 21 ga Yuli, 2018.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa har yanzu Yakubu ya na jiran Majalisar Dattawa ta amince da sabon naɗin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi masa a ranar 27 ga Oktoba, a karo na biyu.

Yakubu ya ce Tsarin Mulki ne ya kafa hukumar kuma an naɗa membobin ta ne bisa wa’adin shekara biyar wanda za a iya sabuntawa a karo na biyu na ƙarshe.

Ya ce: “Wannan na nufin cewa wa’adi na da na Kwamishinoni biyar na farko da aka naɗa ta ƙare a yau.

“Kamar yadda ku ka sani, an riga an bayyana sabunta naɗi na a matsayin Shugaban Hukumar, bisa amincewar Majalisar Dattawa.

“Aikin mu a matsayin manajojin gudanar da zaɓe ya na buƙatar mu bi doka da ƙa’idoji.

“A wajen yin hakan, tilas ne mu nuna tsantar girmamawa ga tare da kiyaye Tsarin Mulki da dokokin Nijeriya.

“Sakamakon haka, ba zai dace ba a gare ni in ci gaba da gudanar da aiki bayan yau ɗin nan, 9 ga Nuwamba, ba tare da amincewar Majalisar Dattawa da kuma sake rantsar da ni ba kamar yadda doka ta tanada.

“Kafin zuwa lokacin da za a kammala bin wannan tsarin na doka, sauran Kwamishinonin Ƙasa sun yanke shawarar cewa AVM Ahmed Mu’azu (ritaya) zai riƙe ragamar hukumar.

“Saboda haka, ina mai farin cikin miƙa ragamar a gare shi a wannan lokaci. Mun yi aiki tare a matsayin guruf ɗaya a tsawon shekaru huɗu da su ka gabata. Don haka, babu wani sabon abu ga kowannen su.”

Yakubu ya yi godiya ga membobin hukumar da kwamishinonin zaɓe na jihohi da sakataren hukumar saboda kyakkyawar hulɗar aiki da ya wanzu a tsakanin su.

Haka kuma ya gode wa darakta-janar na Makarantar Harkokin Zaɓe (Electoral Institute) da daraktoci, membobin sashen aiwatarwa, shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da aka tura su zuwa INEC da dukkan ma’aikatan hukumar da ke dukkan faɗin ƙasar nan. Ya ce, “Ina sa ran ci gaba da aiki tare da ku.”

Shi dai AVM Mu’azu, wanda shi ne kwamishinan ƙasa mai kula da Hukumar Karɓar Bayanan Kwangila a INEC, ya yi alƙawarin riƙe ragamar hukumar bakin iyawar sa har zuwa lokacin da majalisa za ta amince da naɗin Yakubu ya dawo bakin aiki a wa’adin sa na biyu.

Mu’azu ya ce nauyin da aka ɗora masa ba sabon abu ba ne a gare shi saboda dukkan kwamishinonin na ƙasa a lokuta daban-daban sun yi shugabancin riƙon ƙwarya na INEC, a duk lokacin da ya tafi aiki a ƙasar waje.

Ya ce, “A tsawon shekaru huɗu da su ka gabata, ya kasance al’adar shugaban cewa a duk lokacin da zai tafi wata ƙasa ya kan ba wani kwamishinan ƙasa riƙon ƙwaryar shugabancin hukumar.

“Ta haka ne dukkan kwamishinonin ƙasa su ka riƙi muƙamin muƙaddashin shugaba. Don haka, a haka ne mu ke kallon tsarin da aka yi a yanzu, ba wani abu daban ba.

“Ina so in tabbatar maku da cewa zan riƙe al’amuran hukumar nan bakin iyawa ta.”

Shi ma a nasa jawabin, wani kwamishinan ƙasa wanda wa’adin sa ya ƙare tare da na shugaban, Mista Solomon Soyebi, ya yaba wa nasarorin da Yakubu ya samu a wa’adin sa na farko.

Soyebi ya yi kira a gare shi da ya ci gaba da ayyukan da ya saba yi idan ya dawo bakin aiki a wa’adin sa na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

65-year-old man arrested for allegedly raping his 85-year-old stepmother in Ekiti

By Lawrence A. - June 18, 2021 The police in Ekiti State have arrested a 65-year-old man, Durodola Kayode Ogundele, of Ayetoro-Ekiti for allegedly forcefully...

KU MURKUSHE YAN TA ADDA..inji masari

KU MURKUSHE YAN TA ADDA..inji masari Daga abdulhadi bawa Kakkabe ta'addanci ta hanyar murkushe 'yan ta'adda da samar da dawwamammen zaman lafiya ga al'umma shi ne...

PRESS RELEASE BABANGIDA ALBABA RECEIVED PTDF SECRETARY.

PRESS RELEASE BABANGIDA ALBABA RECEIVED PTDF SECRETARY. by Aminu magaji Idris The Rector, Katsina State Institute of Technology and Management Dr. Babangida Abubakar Albaba, has received the...

Babu wanda zai bar jami’a saboda bai biya kuɗin makaranta ba -Farfesa Muhamad Sani Tanko

Babu wanda zai bar jami'a saboda bai biya kuɗin makaranta ba – Farfesa Muhammad Sani Tanko, Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna ya kawar da tsoron da iyayen...

Police Arrest 60-Year-Old Man Conveying Rifles In Car Bonnet

A 60-year-old man, Umar Muhammed, was arrested while conveying firearms across the country. The suspect uses his vehicle to transport rifles concealed in the bonnet...
%d bloggers like this: