Ganduje Ya kwace lasisin ginin nan da ya rushe na kasuwar waya ta beirut
inda ya bada umarnin a mayar da wurin filin parking din motoci
Ya kuma kafa kwamiti domin binkice da hukunta wadanda sukayi ginin ba bisa ka’ida ba
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya bada umarnin ne yayin da ya kai ziyarar jaje ga yan kasuwar tare da mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.
Gwamna Ganduje yayi kira ga dukkanin masu gine-gine da su tabbatar sunyi bisa cika dukkan ka’idoji domin kiyaye rayuka da dukiyoyi al’umma.
Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin sa ba zata zuba ido wasu masu son zuciya suna ganganci da dukiya da kuma rayukan al’ummar sa ba.
Aminu Dahiru
SSA Photography 📸
31st August, 2022